Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Raboon Kayan Abinci Ga Magidanta A Zamfara
- Katsina City News
- 21 May, 2024
- 317
Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon tan 42,000 na kayan abinci daban-daban ga marasa galihu a Zamfara.
An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a ranar Litinin a ofishin Kwamishinan Harkokin Jinƙai na Jihar Zamfara da ke Gusau, babban birnin jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA, ta miƙa wa gwamnatin jihar kayayyaki daban-daban domin rabawa ga marasa galihu.
A cewar sanarwar, Dakta Ishaya Chonoko, Daraktan Hukumar NEMA na shiyyar Arewa maso Yamma, ya wakilci Darakta Janar na Hukumar, Hajiya Zubaida Umar a wajen bikin rabon.
A yayin jawabinsa, Gwamna Lawal ya bayyana cewa rabon kayayyakin ya zo a wani muhimmin lokaci da mutane ke fuskantar ƙalubale saboda ayyukan ’yan fashin daji da kuma tasirin manufofin da aka ɓullo da su a baya-bayan nan da nufin ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce, “Ina miƙa godiyata ga shugaban ƙasa bisa jajircewarsa na kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro, domin idan ba tare da wannan ƙuduri ba, ba za a iya samun nasarori masu ma’ana a kowane fannin da ke taimakawa wajen cigaba ba. Babu shakka wannan taimako zai samar da agajin da ake buƙata ga waɗanda suka ci gajiyar shirin tare da bayar da goyon baya ga ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke ci gaba da yi a wannan fanni.
“Wannan yunƙuri na Gwamnatin Tarayya zai haɗa da ƙoƙarin da gwamnatina ke yi na magance matsalar ’yan bindiga da ta daɗe a jihar tare da samar da tallafi ga al’ummarmu.
“Tun lokacin da na hau mulki a matsayina na gwamna, na ci gaba da yin aiki tuƙuru domin samun goyon bayan yaƙi da ’yan bindiga da tallafa wa marasa galihu a faɗin jihar nan, musamman mata da yara da kuma tsofaffi. A madadin al’ummar Zamfara nagari, ina miƙa godiyata ga Gwamnatin Tarayya bisa wannan da sauran ɗimbin tallafi da ake baiwa jihar mu.
“Ba sai an faɗa ba, waɗannan kayayyaki za su taimaka matuƙa wajen rage wahalhalun abinci da mutanenmu ke fuskanta. Don haka, ina kira ga waɗanda ke karɓar kayan da su yi amfani da su yadda ya kamata.
“Da waɗannan jawabai, ina mai farin ciki a madadin gwamnati da al’ummar jihar Zamfara, na karɓi tan 42,000 na kayayyakin abinci iri-iri tare da ƙaddamar da rabon kayayyakin ga marasa galihu mazauna jihar Zamfara.
“Allah Maɗaukakin Sarki ya ci gaba da baiwa dukkan ƙoƙarinmu da nasara a matakai daban-daban na gwamnati. Ya kuma dawo mana da zaman lafiya a tsakanin mutanenmu. Allah ya sa waɗannan kayayyaki su amfana sannan su samar da agajin gaggawa ga marasa galihu a faɗin jihar.”