Muna Samun Gagarumar Nasara Kan 'Yan Bindiga A Zamfara, Babu Inda Aka Sace Mutum 500 -Hedikwatar Tsaro
- Katsina City News
- 18 May, 2024
- 391
Hedikwatar tsaro ta ƙasar nan (DHQ) ta bayyana cewa tana samun Gagarumar nasara a yaƙin da ta ke yi da 'yan Bindiga a jihar Zamfara, inda kuma ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa, cewa wai an sace mutum 500 a Ƙaramar Hukumar Zurmi ta jihar, ta ce, wannan ƙarya ce tsagwaron ta, wacce wasu maƙiya zaman lafiyar jihar ke yaɗawa.
Daraktan yaɗa labarai na rundunar Sojin, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a yau Juma’ar nan a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, inda ya ce a zahiri an sace mutane huɗu ne kawai, saɓanin alƙalumman da ake yaɗawa.
Janar Buba ya jaddada cewa dakarun Operation Hadarin Daji suna aiki ne a cikin wani yanayi mai cike da ƙalubale, inda ya zama dole su magance haƙiƙanin gaskiya da kuma bayanan ɓata-gari, musamman daga shafukan sada zumunta.
Ya ƙara da cewa, maganar mutane 500 da aka yi garkuwa da su, wani ƙarin gishiri ne, inda aka tabbatar da sace mutane huɗu ne kawai.
Buba ya kuma ba da tabbacin cewa sojojin za su ci gaba da mai da hankali wajen fatattakar ƴan ta’adda, inda tuni aka kawar da shugabannin ƴan ta’adda da dama.
Haka zalika ya ce, sojoji na haɗa kai da jami’an tsaro da al’ummar jihar Zamfara domin inganta tsaro, duk da ƙalubalen da ake fuskanta, domin cikin taimakon Allah, sojoji na da ƙarfin faɗa da ƴan ta’adda, inda suke samun nasarori a ayyukansu.