Ministan Yaɗa Labarai ya yi alƙawarin tallafa wa gidan Rediyon EFCC
- Katsina City News
- 18 May, 2024
- 389
Daga WAKILIN MU
.
.
MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi alƙawarin tallafa wa manufofin gidan rediyon Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai suna EFCC Radio.
Idris ya bayyana hakan ne a wurin taron ƙaddamar da gidan rediyon da ke kan lamba 97.3 a zangon FM wanda aka yi a hedikwatar hukumar a Jabi, Abuja a ranar Alhamis, 16 ga Mayu, 2024.
Ministan ya ce: "Ku tabbatar da cewa a matsayi na na Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, zan yi duk abin da zan iya don tallafa wa manufofin ku."
Kafin yin wannan iƙirarin, ministan ya bayyana jin daɗin sa “da halartar wannan bikin ƙaddamar da sabuwar hanyar sadarwa a Nijeriya, wato EFCC Radio 97.3 FM.
“Dole ne in ce abin farin ciki ne sosai ganin ɗaya daga cikin manyan hukumomin tabbatar da doka da oda a ƙasar nan na ƙara faɗaɗa hanyoyin sadarwar jama’a da gudanar da ayyukan su ta hanyar kafa gidan rediyon FM.
“A matsayin ta na hukumar da ke fuskantar jama’a, haƙiƙa yana da matuƙar muhimmanci Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC) ta tsara labaran da ke tattare da duk wani muhimmin yaƙi da ake yi da cin hanci da rashawa a ƙasar mu a tsanake da dabaru.”
Ya kuma yi alƙawarin cewa, “Tare da yin aiki ta hannun Hukumar Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC), za mu kuma tabbatar da cewa mun ƙarfafa gwiwar sauran hukumomin gwamnati da abin ya shafa su yi haka, tare da bayar da gudunmawa wajen faɗakarwa da wayar da kan jama’a.”
A cewar ministan, “Ajandar mu ta biyu cikin 5 a Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ita ce inganta manufofi da tsare-tsare na Gwamnatin Tarayya, kuma ina farin ciki da cewa a yanzu mun samu wannan sabuwar abokiyar hulɗa, EFCC Radio 97.3. FM, wacce za ta taimaka mana wajen cimma wannan manufa.
“Abu na farko na waccan ajandar mai ƙunshe da abubuwa biyar shi ne dawo da amana a harkokin sadarwar jama’a a Nijeriya.
"Ina so a kan haka, in umarci masu gudanarwa da ma'aikatan wannan sabuwar tashar, da su yi ƙoƙari su yi aiki a kowane lokaci bisa ƙa'idoji na aikin watsa labarai da aikin jarida.
“Ku ne abokan hulɗar mu masu ƙima yayin da muke neman sake ginawa da dawo da yardar al’ummar Nijeriya kan bayanan da ke fitowa daga Gwamnatin Tarayya.
"A kan haka, bari in sake taya Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC) murna, kan wannan rawar da ta taka. Ina yi maku fatan alheri yayin da kuka fara aiki gaba ɗaya."
Hoto:
Alhaji Mohammed Idris yana jawabi a wajen ƙaddamar da EFCC Radio
Ana tattaunawa da Ministan a sabon gidan Rediyon EFCC