DAN LAWAN KATSINA YA YI MA SHEMA TAWAYE
- Katsina City News
- 18 May, 2024
- 696
....Akan gwamnatin Masari a hirarsa da BBC.
Daga Danjuma Katsina @Katsina Times
Alhaji Hamisu Gambo Dan lawan Katsina, gogaggen Dan siyasa kuma shugaban rukunin gonaki da makarantun Dan lawan dake Katsina ya barranta kanshi da hirar da shema yayi da BBC wanda ya nuna bai San aikin da gwamnatin Masari tayi ma al ummar Katsina a shekaru takwas din da tayi tana mulki.
Alhaji Hamisu Gambo Wanda ya kasance tare da shema a duk halin da ya shiga a lokacin da hukumar EFCC na tuhumar sa, shema. Akan kudaden kananan hukumomin Katsina da kuma na sure P.
Alhaji Hamisu Gambo wanda aka sanshi na cikin shuhada u na shema a da. Ya bayyana ma Babban editan jaridun Katsina Times cewa, sam shema baiyi ma gwamnatin Masari adalci ba a wannan hirar tashi da BBC.
Alhaji Hamisu Gambo yace, Ni da Abdul aziz Mamman mai turaka, Muka yi ruwa mukayi tsaki, Masari ya amshi shema a bisa maslahar Katsina da al ummar ta.
Masari ya amshi shema kamar yadda ake ma Wanda ya musulunta sabon tuba a musulunci, watau da Wanda ya shigo yanzu da Wanda ya Dade duk daya suke.
Hamisu Gambo yace duk wani halasci da akeyi,Masari yayi ma shema.hatta wasu ayyukan karshen gwamnatin ta Masari da aka kaddamar babu Wanda ba a gayyaci shema ba.
Hamisu Gambo yace, Muke tare da shema kafin mu kaishi ga Masari sai da muka gamsar dashi duk ayyukan Alheri na wannan dattijon Masari kuma ya gamsu bisa hujja.
Hamisu Gambo, yace Masari shine ya hada Shema da gwamnan Katsina na yanzu Alhaji Dikko Radda,yace suyi aiki tare.
Hamisu Gambo yace, Sam Shema baiyi adalci ba,yace bai San me gwamnatin Masari tayi ba.Anan sai Hamisu Gambo ya kara jaddada cewa baya tare da shema anan.
Hamisu Gambo ya kara da cewa, gwamnatin Masari babu halasci da ba tayi ma shema da mutanen shi.
Hamisu Gambo ya ce Maganganun Shema babu dattaku a cikin su.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 080 577777762