AN CETO ALHAZAN KATSINA DAGA BASU BABBAR JAKA MAI 32kg DAGA NAJERIYA.
- Katsina City News
- 16 May, 2024
- 781
...An jinjina ma gwamnan Katsina da Amirul hajj.
@ Katsina Times
Amirul Hajj na Katsina Alhaji Tukur Ahmad jikamshi ya Ceto Alhazan Katsina daga kokarin dankara masu babbar jaka mai 32kg daga Najeriya zuwa kasa mai tsarki.
Kwamitin da Amirul hajj ya kafa karkashin mai Shari a Bawale Wanda yake yana cikin tawagar Amirul hajj na aikin hajjin wannan shekarar ta 2024.
Kwamitin ya Kira dan kwangilar jikkunan Wanda ya shaida masa kai tsaye rashin amincewar gwamnatin Katsina da al ummar ta na Cogen da ake neman yi ma mahajjatan Katsina da dankara masu daukar jaka daga Najeriya mai 32kg.
Dan kwangilar ya amince ya kai ma mahajjatan Katsina jikkunan su har makka, kamar yadda kwangilar da aka bashi ta nuna. Sannan dankwangilar yayi yarjejeniya da kamfanin Maxair ya kai masa jikkunan zuwa makka
Wannan yarjejeniyar an yi ta a rubuce da sanya mata hannu tsakanin Dan kwangilar jikkuna da kamfanin Maxair da kuma hukumar alhazan jahar Katsina.
Da wannan mataki an kawo karshen wannan matsalar da tana iya kawo cikas ga tafiyar Alhazan Katsina zuwa aikin hajji.
Jaridun Katsina times sun ji ra ayin wasu mahajjatan da abin ya shafa wadanda sukayi ta kwarara addu a ga Amirul hajj Alhaji Tukur Ahmad jikamshi akan wannan tsayin daka da yayi.
Wani abu da jaridun Katsina Times suka gano gwamnan Katsina ya dauki aikin hajjin na bana da muhimmacin da duk abin da hukumar alhazan Katsina suka nema don aikin ya amince masu kuma ya basu kudin dari bisa dari cif.
Jaridun Katsina Times sun gano gwamnan na Katsina ya sanya ido da kunne sosai akan yadda za a aiwatar da hajjin bana 2024 cikin nasara.
Wannan ya sanya ya nada Alhaji Tukur Ahmad jikanshi Amirul hajj, Wanda a tarihin shi bai San wasa a aiki ba.
Shine ( Tukur Jiamshi) tare da Sani Abubakar lugga suka ajiye aikin mukaman su na kwamishinoni a 1994 a zaman mulkin soja da suka ga ana yin ba dai dai ba.kuma anki gyarawa
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
www.taskarlabarai.com
07043777779 080577777762