Kotu Ta Ce ‘Yan Sanda Su Biya Diyyar Naira Miliyan 200 Bisa Kashe ‘Yan Shi’a a Soba
- Katsina City News
- 14 May, 2024
- 357
Ta ce matakin da ƴan sanda suka ɗauka haramtacce ne a kundin tsarin mulkin ƙasa
Sahara Reporters Hausa
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ta umurci hukumomin ƴan sanda da su biya zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 200 ga iyayen ‘yan Shi’a guda biyu da jami’anta suka kashe a lokacin da suke gudanar da muzaharar Ashura a ranar 28 ga watan Agustan 2022 a garin Soba dake ƙaramar hukumar Soba ta jihar Kaduna.
Mai shari’a Hawa Buhari, a cikin hukuncin da ta yanke, ta tabbatar da take haƙƙin waɗanda aka kashe kamar yadda aka tanadar a cikin sashe na 33, 38, 39, 40, 42 da 46 na kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima); Ɓangare na 4,8,10, 11 da 12 na Dokar Yarjejeniyar Afrika (African Charter) kan ƴancin ɗan Adam da Jama'a (wacce aka sanya wa hannu aka ɗabbaƙa) ta shekarar 2004 da kuma Doka 1,2,3,4 da Oda ta 11,12, na Ƙa'idojin Aiwatar da Haƙƙin Bil-Adama na shekarar 2009”.
Alƙalin kotun ta ce dole ne a biya adadin kuɗi har Naira miliyan 100 ga kowanne iyayen waɗanda aka kashe, inda za a biya jimillar naira miliyan 200 ke nan a matsayin diyya da kuma ɓarnar da aka aikata, sannan kuma har wala yau za a biya ribar kashi 10 cikin 100 a duk shekara har sai an biya kuɗin baki ɗaya.
Mai shari’a Buhari, a hukuncin da ta yanke a ranar 13 ga watan Mayun, 2024, - kamar yadda ɗaya daga cikin lauyoyin masu ƙara ya bayyanawa manema labarai jim kaɗan bayan fitowa kotun- ta haɗa ƙararraki biyu (consolidation) dake gabanta waɗanda makusantan waɗanda aka kashe suka shigar daban daban a kotun.
“Bayan da lauyoyi suka tabbatar da ƙarar ta su tare da gabatar da shaidu kuma Kotu ta yi nazari hujjojin masu ƙara da kuma waɗanda ake ƙaran, sai ta yanke hukunci ta kuma bada umurni kamar haka:
“An haɗa ƙara mai lamba: FHC/KD/CS/142/2022, da mai lamba: FHC/KD/CS/144/2022.
“Dole waɗanda ake ƙara su biya kuɗi Naira miliyan 100,000,000.00 (Naira Miliyan Ɗari) ga kowanne mai ƙara a matsayin diyyan kisan da aka yi tare da biyan ribar kashi 10% a duk shekara har sai an biya kuɗin duka.
“Waɗanda aka shigar da su ƙararrakin dole ne su ba da haƙuri a rubuce ga waɗanda suka shigar da ƙara a ɗaya daga cikin jaridun ƙasa da ke fitowa a kowacce rana saboda take haƙƙin su da aka yi,” in ji ta.
Idan za a iya tunawa cewa a gaban Babban Kotu Tarayya ta 2 da ke Kaduna, ƙarar mutane biyu ne da suka haɗa da; Ahmad Sa'ad da Iliyasu Bashir kan kashe masu ƴaƴan su da jami'an tsaron ƴan sanda aka kuma ba ƙararraki lambobi kamar haka: FHC / KH/ KD/ 142/2022, FHC / KH/ KD/ 144/2022.
Takardar shigar da ƙarar sun yi zargin cewa a ranar 28 ga watan Agustan 2022, jami’an ‘yan sandan Nijeriya suka harɓe 'ya'yansu: AMINU ABDULKADIR da MUBARAK ILIYASU a lokacin da suke gudanar da ibadarsu ta muzaharar Ashura a garin Soba.
Sun kai ƙarar Sufeto-Janar na ’yan sanda (IGP), Mataimakin Sufeto-Janar na ’yan sanda na shiyya ta 7, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, da kuma Daniel Pom, jami'in ƴan sanda (DPO), na gari Soba (a lokacin), a matsayin masu amsa ƙara na 1 zuwa na 4.
Masu ƙarar a cikin ƙarar da suka shigar a ranar 26 ga Satumba, 2022 tare da kuma gabatar da ita a ranar 26 ga Satumba, 2022, ta hannun tawagar lauyoyinsu sun gabatar da buƙatu guda bakwai.
Sun nemi da a bayyana cewa harbe da kashe AMINU ABDULKADIR da MUBARAK ILIYASU, a lokacin gudanar da muzaharar su ta addini ya saɓawa doka, ya kuma saɓawa tsarin mulkin ƙasa, sannan ya kuma tauye haƙƙinsu na rayuwa kamar yadda sashe na 33 na kundin tsarin mulkin 1999 da kuma Doka ta 4 na Yarjejeniyar Afirka kan Haƙƙoƙin Ɗan Adam da taron jama'a mai lamba Cap A9 LFN na shekarar 2004 ya tabbatar.
A don haka masu ƙarar ta hanyar lauyoyinsu suka roƙi kotun da ta umurci waɗanda ake ƙara baki ɗaya da su biya naira miliyan 200 ga kowannensu saboda tauye haƙƙin ‘yan uwansu da suka kashe.
Haka kuma sun nemi kotun ta bayar da umurni ga waɗanda suke ƙara da su rubuta takardar bayar da haƙuri tare da bugawa a cikin jaridun ƙasarnan guda biyu da ke yawo a arewacin Nijeriya.
Sai dai waɗanda ake ƙara, a cikin martanin su na farko mai kwanan watan 8 ga Nuwamba, 2022 wanda suka gabatar duk a wannan kwanan wata sun nemi da kotun ta soke ƙararrakin. Bugu da kari suka ce kotun ba ta da hurumin sauraron waɗannan ƙararrakin.
Sai dai kuma mai shari’a Buhari ta amince da hujjojin martani lauyoyin masu ƙara na cewa tanada hurumin sauraren ƙarar. Saboda haka ta yanke hukunci kan shari'ar.