ANA NEMAN WAHALAR DA ALHAZAN JAHAR KATSINA ...Saboda Jikkuna masu 32kg.
- Katsina City News
- 13 May, 2024
- 664
Muazu Hassan @ Katsina Times
Jaridun Katsina Times sun samu wasu takardu akan kwangilar Jikkunan Alhazan jahar Katsina.
Wata takarda da jaridun suka samu ita ce wadda dan kwangilar jikkunan kamfanin Loya Bags ke godiya da murnar an biya shi kudin kwangilar shi baki daya dari bisa dari tun kafin ya fara aikin, wanda wannan Biyan kudi baki daya ya saba ma dokar kaidar bada kwangila da ake da ita.
Dan kwangilar ganin ya amshe kudin shi daga hukumar alhazai sai kuma yazo da wani tsarin da ba a taba kamar shi ba.
Shine zai ba Alhazan katsina manyan jikkunan su masu 32kg su tafi dasu a hannu.
Wannan ba a taba yin haka ba, tunda ake aikin Hajji. Dan kwangilar jikkuna shine ke kai manyan jikkunan alhazai makkah kuma ya kai masu har masauki.
A wannan shekarar dan kwangilar sai ya rubutama hukumar NAHCON ta kasa cewar yana son Alhazai su amshi jikkunan su daga Najeriya. Kamar yadda jaridunmu suka ga wasikar, Nahcon ta bashi amsa cewa wannan ba hurumin su bane hurumin jihohi ne yaje ya tattauna da jihohin da yayi ma aikin jikkunan in sun amince.
Binciken jaridun mu sun tabbatar an fara kawo jikunnan alhazan katsina amma duk manya ne masu 32kg.
Mun samu hotunan jikkunan kamar yadda aka Doro su a manyan motoci duk manyan jikkuna ne.
Mun samu takardar da aka kawo jikkunan a hukumar alhazai ta katsina, a takardar (Invoice) an rubuta jikkuna 8kg amma jikkunan da aka sauke 32kg ne.
A kaida karamar Jaka mai 8kg ake ba Alhazai daga Najeriya, dan kwangila ya kai masu Babbar Jaka mai 32kg har masaukansu a makkah. Me yasa bana ta chanza? "Daukar Babbar Jaka daga Najeriya ga alhaji za a wahalar dashi Musamman sabon Alhaji." Shine ra a yin wasu tsaffin alhazai da muka samu.
"Shin dan kwangilar zai maido ma Alhazan katsina kudin su na kai jikkunan su Saudi Arabia ne? Ko ko zai maido ma hukumar Alhazai ta Jahar katsina ne? Ko wasu ne zasu amfana da wannan rarar da ya samu?"
Wannan shine tambayar da wasu da muka ji, ra a yinsu suke tambaya.
Mun yi magana da Shugaban hukumar Alhazai ta jahar Alhaji Inusa Dankama yace shi ba zai gasgata ko ya karyata ba
Amma in muna da hujja akan labarin mu muna iya cigaba da buga labarin.
Katsina times: wwwkatsinatimes.com