Adabin Abubakar Imam: Gudunmowar Malumfashi Ibrahim
- Katsina City News
- 12 May, 2024
- 354
Daga farfesa Abdalla uba adamu
Bana jin akwai wanda ya yi taza da tsifa a kan littafin “Magana Jari Ce” kamar Farfesa Ibrahim Malumfashi. Ya yi digirin digirgir a kan Magana Jari Ce, wallafar marigayin marubuci, Alhaji Abubakar Imam (1911-1981, wanda aka buga a 1937. Ka ga kenan a lokacin mawallafin na da shekaru 26 a duniya. Daga nan ma kawai, wannan tabbas ya nuna irin basirar da Allah ya ba wa Abubakar Imam, wacce kuma ta cancanci a yi nazari a kan shi.
Ko mai za a ce game da Magana Jari Ce, littafi ne mai ɗimbin muhimmanci a tarihi a adabin Hausa, ba ma a Najeriya ba, a ko’ina a duniya. Saboda muhimmancin littafin, an fassara shi zuwa Larabci a University of Cairo, Egypt, da kuma University of Warsaw, Poland.
A wata ziyarar malanta da na kai jami’ar Cairo, na sayi littafin fassarar Magana Jari Ce da Larabci a shagon sayar da littattafan su ranar 3 ga Janairu 2005. Kai, har ma na samu mun zanta da wanda ya jagoranci fassar, Mustafa Hijazi As-Sayyid (wanda a lokacin ya yi ritaya daga jami’ar, bayan wani lokaci Allah Ya yi masa rasuwa). Wanda kuma ya gabatar da fassarar shi ne Mahmud Fahmi Hijaz (ya rasu 2018). Dukkanin su sun taɓa zama a Kano, a gidan baƙin ziyara (akasari Turawa) da ke dab da Sabuwar Ƙofa, a cikin garin Kano.
Su biyun duk sun kuma fassara littattafan adabin Hausa na farko a ƙarƙashin Turawan mulkin mallaka zuwa Hausa. Waɗannan kuwa su ne “Shaihu Umar”, “Ganɗoki”, “Ruwan Bagaja”, da “Jiki Magayi”. Da ba su samu “Idon Matambayi” ba, sai suka fassara “Iliya ɗan Maikarfi” a madadi, suka haɗa da sauran! Amma a bangon littafin fassarar haɗaɗɗun littattafan, sun kira littafin da ‘'Ma'asaatul Abid' wa Qisas ukhra’, a takaice, bala’in da ke tattare da cinikin bayi, wanda kuma shi ne jigon littafin farko da suka fassara, watau “Shaihu Umar”.
Sannan kuma an fassara Magana Jari Ce cikin harshen Polishanci a Jami’ar Warsaw. A lokacin ina Jami’ar Warsaw a matsyin farfesa mai kawo ziyara, a ƙarƙashin tallafin European Union. Na bayar da ƴar gudunmowa wajen haɗa masu fassarar da kuma waɗanda za su bayar da iznin a yi fassarar. A ƙarshe dai, bayan an ci kwakwa, littafin ya fito ana sayar da shi a Amazon. Babban dalilin fassarar zuwa Polishanci shi ne nuna gwanintar Abubakar Imam ga mutanen Poland. Nake jin kuma shi kaɗai ne marubucin Hausa da aka yi wa haka.
Saboda haka nazari akan littafin Magana Jari Ce babbar gundunmowa ce ga ilimin adabin Hausa, wanda har yanzu babu wanda ya yi da zurfi da kuma kaifin da farfesa Ibrahim Malumfashi ya yi.
Babbar matsalar ita ce akasari irin wannan gudunmowar a cikin ɗakin karatun da a ka yi rubutun a ke barin su. Sai an ci kwakwa kafin ma a ƙyale ka samu ganin su. Amma sanin muhimmacin aikin da ya yi domin amfanar al’umma, Ibrahim Malumfashi, ya juya kundin digirin na sa (wanda ya samu a 1999) zuwa littafi wanda ya kira “Adabin Abubakar Imam”. Duk martabar da ke cikin digirin an fito da ita fes a littafin, wanda shi ne shaidar sahihancin digirin digirgir, watau gudunmowa ga fagen sani (contribution to knowledge).
An buga shi shekaru goma bayan gama digirin, watau a 2009. Na yi sa’a, ana buga shi Ibrahim ya ba ni kwafe ranar 14 ga Afrilu 2009 tare da jinjinawa (compliment). Wannan littafin yana daga cikin manyan littattafan da ba sa barin iro na.
Babbar tambayar (wacce ta yi sababin wannan rubutun) ita ce: a ina za a same shi? Sannan kuma akwai abin da na kira ‘acibilistic’ kwafe? Farfesa Malumfashi Ibrahim dai shi zai iya ganar da mu inda za a samu wannan littafin mai muhimmancin tarihi a adabin Hausa. Kuma zai yi kyau in da zai zuya shi zuwa harshen Turanci saboda ƴan ƙasarnan su san irin basirar da Allah Ya bawa Hausawa, a daina raina su a fage sani da ilimi. Ni dai ina da kwafe, Alhamdulillah.
Suma na Larabcin ina da su a zahiri, ba eCopy ba. Kuma bana ba da aro!
Illus.