Ƴanbindiga Sun Kashe Ma’aikacin Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji Ta Kasa (FIRS) A Abuja
- Katsina City News
- 12 May, 2024
- 442
Wasu ’yan bindiga sun kashe wani matashi mai suna Khalid Bichi a Unguwar Maitama da ke Abuja a ranar Juma’a.
Bichi, wanda aka ruwaito cewa ma’aikaci ne a Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS) ya yi gamo da ajalinsa ne da misalin ƙarfe 9 na dare a lokacin da ya fita sayen abinci.
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa maharan sun harbi matashi sau dama kafin su ranta a na kare.
Bayanai sun ce bayan faruwar lamarin, an garzaya da matashin Babban Asibitin Maitama, inda aka tabbatar da rasuwarsa.
Tuni dai an binne mamacin bayan jana’izarsa da aka gudanar da ƙarfe 1:30 na ranar Asabar a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja.
Majiyoyi sun ya tabbatar da cewa marigayin wanda ya shahara da sunan @KhalidBichi musamman a shafin X (Twitter) yana da alaƙa da manyan ’yan siyasa a ƙasar.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta ce suna ci gaba da gudunar da bincike a kan lamarin.
Dare Adekanmbi, mai ba da shawara na musamman kan harkokin sadarwa ga Shugaban hukumar ta FIRS, Zacch Adedeji, ya ce ba su da wani cikakken bayani a kan lamarin da a yanzu haka yana hannun hukumar ’yan sanda.
Sai dai ya ce hukumar tana cikin jimamin rashin ɗaya daga cikin ma’aikata yayin da kuma take miƙa saƙon ta’aziyya zuwa ga mata da kuma ’yan uwan mamacin.
Majiya: Trust Radio