SIYASA ROMON JAƁA: Dalilai 10 Suka Harzuƙa Shema Ficewa Daga PDP, Ya Rungumi Jam'iyyar APC
- Katsina City News
- 10 May, 2024
- 532
An daɗe ana jiran jin sanarwar komawar tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema cikin APC, domin ya daɗe da raba hanya da PDP, tun kafin zaɓen 2023.
Shema ya riƙa sukar jam’iyyar PDP wadda a ƙarƙashin ta ya yi Gwamnan Katsina daga 2007 zuwa 2015. Ya riƙa caccakar PDP daidai fara kamfen na zaɓen 2023.
Shi ya sa ba abin mamaki ba ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya kayar da Atiku Abubakar na PDP, Shema ya yi gaggawar fitowa ya taya shi murna, kuma ya yi kira ga Atiku Abubakar ya haƙura, ya rungumi ƙaddara.
Kafin nan jam’iyyar PDP ta dakatar da wasu jiga-jigan ta da ta yi zargi da yi mata ‘anti-party’, ciki har da Shema.
Ganin haka, sai Shema ya nemi a janye dakatarwar da aka yi masa, ko kuma ya fice daga jam’iyyar PDP. Jin haka sai PDP ta janye dakatarwar da ta yi masa.
A fili take cewa Shema ya yi ƙulle-ƙullen kayar da PDP a zaɓen 2023 a Katsina, saboda dalilai da yawa.
Kakakin Yaɗa Labaran Shema mai suna Olawale Oluwabusola, ya bayyana cewa “an maida Shema saniyar-ware, an jefar da shi a sahun baya a PDP.”
Shema ya fara shiga cikin taskun PDP tun a cikin 2019, inda Yakubu Lado ya ƙwace kambun faɗa-a-jin PDP a Katsina, bayan ya kayar da ɗan takarar Shema a zaɓen fidda-gwani. Sai dai Lado ya ɗauki makusancin Shema, wato Salisu Majigiri a matsayin mataimakin takara, amma Gwamna Aminu Masari ya kayar da su da ya tsaya a ƙarƙashin APC.
A zaɓen 2023, Lado ya sake yin nasarar zama ɗan takarar gwamnan Katsina a ƙarƙashin PDP. To amma sai ya ƙi ɗaukar makusantan Shema ko ɗaya a matsayin mataimakin takara, ya ɗauki Ahmed ‘Yar’Adua, wanda wasu ‘yan PDP suka yi ba shi da tasiri a zukatan mutanen karkara.
Abin da Lado ya yi ya sa Shema da jama’ar sa suka janye jiki daga goyon bayan PDP.
Wani dalili da ya sa Shema ya yi wa PDP ‘anti-party’ a zaɓen 2023, shi ne shigar Mustapha Inuwa cikin PDP, bayan ya raba hanya da Gwamna Masari, wanda kafin ɓaɓewar su, shi ne Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina.
Inuwa ya fice daga APC bayan Gwamna Masari ya ƙi tsaya masa ya samu tikitin takarar gwamna, sai aka bai wa Dikko Raɗɗa.
Shi kuma Shema ba ya shiri da Mustapha Inuwa, a tsawon shekarun da ya yi na gwamna. Kafin nan kuwa su biyu ɗink sun yi aiki tare a ƙarƙashin gwamnatin marigayi Umaru Musa ‘Yar’Adua, a lokacin da yake gwamnan jihar Katsina.
Mustapha Inuwa ya fice daga PDP ya koma APC a 2015, ya haɗe da Masari, suka kayar da PDP.
Bayan Inuwa ya koma PDP a zaɓen 2023, ya haɗe da Yakubu Lado, lamarin da ya dagula Shema a PDPin Katsina.
“Sai Shema ya ga ba zai ƙara shan inuwar lema tare da Mustapha Inuwa ba, sai ya ga har gara ya fice, ya bar masu PDP ɗin ɗungurugum.
Daga nan sai Shema ya raɓi Dikko Raɗɗa, wanda a lokacin shi ma neman bangon jingina yake yi a APC, domin ƙara ƙarfi, saboda haɗewar Mustapha Inuwa da Yakubu Lado a PDP babbar barazana ce a gare shi.
Mustapha ya san ƙabli da ba’adin siyasar mutanen karkara, kuma ya na tare da su. Kenan samun Shema ya samar wa Raɗɗa sassaucin kaifin su Lado da Inuwa a siyasance.
Yayin da Shema ya sakar wa Raɗɗa dakarun siyasar sa su na yi masa aiki, Shema ya tsaya a PDP bai fice ba tukunna, amma dai an yi ta zargin cewa mutanen Shema sun zaɓi Raɗɗa a zaɓen 2023.
Janye Ƙarar Neman Naira Biliyan 11 Da Gwamnatin Katsina Ke Wa Shema:
Kafin zaɓen 2023, Gwamnatin Jihar Katsina ta ba-zatar janye ƙarar da ta gurfanar da Shema, inda take neman Naira biliyan 11 da take zargin ya wawura, shi da wasu a zamanin mulkin sa. Tun cikin 2023 ake dambarwa a kotu, amma shi Shema ya sha nanata cewa bai ci kuɗin ba, a cewar sa bi-ta-ƙulli ne kawai Gwamnatin Aminu Masari ta riƙa yi masa.
Bayan janye ƙarar Shema da gwamnatin Katsina ta yi, an naɗa riƙaƙƙen makusancin siyasar Shema, Bashir Tanimu muƙamin Kwamishinan Harkokin Kuɗaɗe, kuma aka naɗa wani makusancin na sa, mai suna Ibrahim Ɗankaba Shugaban Hukumar Tsaftace Ruwa (STOWASSA).
Wani abu da ya ƙara tunzira Shema ficewa daga PDP, shi ne irin yadda ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya maida shi ‘shakulatin-ɓangaro’ a lokacin kamfen.
Waɗanda suka san abubuwan da suka faru a lokacin, sun ce Atiku da PDP ko sanar da Shema za a yi kamfen a Katsina ba su yi ba, ballantana ma a gayyace shi.
Ficewar Shema daga PDP zai iya kawo ƙarshen rikicin jam’iyyar a Katsina, inda a yanzu haka shugabannin riƙo ke riƙe da jam’iyyar a jihar.
To sai dai kuma ko shakka babu ‘jonewar’ da Shema ya yi a cikin APC, zai ƙara nesanta PDP daga samun nasarar kama kujerar gwamnan jihar Katsinawan Dikko.
Majiya: Premium Times Hausa