Kungiyar Manoma Ta AFAN Zata Jagoranci Gangami Akan Dashen Itatuwa A jihar Katsina. Inji Gwajo-gwajo
- Katsina City News
- 09 May, 2024
- 416
Shugaban kungiyar Manoma ta AFAN ya bayyana cewa kungiyar su zata jagoranci gangami domin karfafa gaiwar al'umma da cewa duk wanda ya sare icce ɗaya dole ya shuka guda uku saboda a cewar sa ta haka za a ƙara samar da itatuwa a jihar Katsina .
Shugaban kungiyar Hon. Ya'u Umar Gwajo-gwajo ne ya bayyana haka acikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Katsina
Kungiyar Manoma ta ƙasa reshen jihar Katsina (AFAN) ta yi kira ga 'ya 'yan ta da su himmatu wajen dasa itatuwa domin hana kwararowar Hamada da zaizayar ƙasa a jihar Katsina
Ya ce babbar matsalar sare itatuwa ita ce, yana haifar da ɗumamar yanayi da zafi da ambaliyar ruwa da zaizayar ƙasa da ka iya shafar noma da manomaa jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya
Hon. Ya'u Umar Gwajo-gwajo ya ƙara da cewa tsofaffi shuwagabannin arewa irin su Amadu Bello Sardaunan Sokoto da sauran sarakunan gargajiya sun shuka itatuwa domin samar da labi da ke hana kwararowar hamada da kuma amfanin da itatuwa ke samarwa al'umma.
Kungiyar Manoman ta nemi gudunmawar gwamantin jihar Katsina domin samun dama da kwarin gwiwa domin yin dashen itatuwa don amfanin manoma da kyautata muhalli.
Kamar yadda ya bayyana cewa shuka itatuwa addinin musulunci ne ya zo da shi, daga Manzon Allah (S) wanda yace akwai lada gwagwaɓa a wajen Allah gobe kiyama.