An kammala Taron Karawa Juna sani na kwana Uku akan Bunkasa Kiwon Lafiya a Katsina
- Katsina City News
- 08 May, 2024
- 500
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Laraba takwas (8) ga watan Mayu 2024 ne a ka kawo karshen taron na Horaswa da karawa juna sani akan sha'anin lafiya da gwamnatin jihar Katsina tare da ma'aikatar Lafiya bisa jagorancin Kwamishinan ma'aikatar Dakta Bishir Gambo Saulawa suka shirya.
Taron bitar na kwanaki uku akan bunkasa sha'anin lafiya da aka gudanar a babban dakin taro na Sakatariyar gwamnatin jihar Katsina, ya tattaro masana da Malaman lafiya a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina inda aka tattauna sha'anin lafiya da hanyoyi ko sabbin dabarun habaka kiwon lafiya a matakai daban-daban.
Masana daga ciki da wajen jihar Katsina sun gabatar da kasidu kuma aka tattauna akansu tare da neman mafita akan harkokin lafiya a jihar ta Katsina.
Tun da farko gwamnan jihar Katsina malam Dikko Umar Radda ne ya bude taron bitar tare da bayyana irin matakan da gwamnatin sa ke dauka don habaka tare da bunkasa sha'anin lafiya a fadin jihar Katsina ta hanyar samar da Asibitoci, Bunkasa Tsaffi da samar da kayayyakin Aiki na zamani don saukakawa.
A wajen Taron an karrama wasu zarata kuma jajirtaccin Mutane don kara masu kwarin gwiwa akan cigaban da suke kawowa a sha'anin lafiya a fadin jihar Katsina.
Mutu nen da aka karrama sun hada da Dakta Umar Mutallab, Alhaji Dr. Bilya Sanda, Dr. Halima Adamu, Farfesa Abdulmumini Hassan Rafindafi. Sai kuma Hajiya Rabi Amadu Kumasi, Janaidu Mamuda 'Yan Tumaki, Farfesa Umar Adamu Katsayal, Ibrahim Muhammad Kaita, Kwamarad Tanimu Lawal Saulawa, Abdulrashid Ibrahim Darma. Sauran sun hada da Dr. Lawal Nura, Abdullah Ahamad, Abdullahi Ahamad Bakori, Aisha Muhammad Mashi da Kabir Salisu.