WASU DAGA CIKIN KOFOFIN KATSINA DA BABU SU YANZU.
- Katsina City News
- 08 May, 2024
- 625
1. Kofar Turmi
2. Kofar Keke
3 Kofar Gazobi
Tarihin kafuwar Kofofin Katsina Yana da nasaba ginin Ganuwar Katsina wadda aka gina wajen karni na 15, a lokacin mulkin Sarakunan Habe.
Ginin Ganuwa alamace ta kafuwar Jamaa'a a wuri daya domin amfanin kowa da kowa. Kuma ana Gina Ganuwa domin a samu tsaro ga Gari ko Kasa. Wannan dalilin yasa lokacin da aka gina Ganuwar Katsina wajen karni na 15 Sai aka Gina Kofofi wadanda suka zagayeta, Kuma aka sa Sarkin Kofa ga kowace Kofa don samun tsaro daga mahara, ko baki. K Daga cikin Kofofin da suka kafu a Katsina akwai Kofar Kwaya, Kofar Marusa, Kofar Yandaka, Kofar Kaura, Kofar Durbi, Kofar Gazobi, Kofar Turmi da sauransu.
Bari mu dauki wadqnda suka dade da bacewa, muyi bayani akansu.
1. Kofar Turmi.
Kofar Turmi Tarihin ta ya nuna tun lokacin Sarakunan Habe akwaita, domin lokacin da Mujahidai suka ci Katsina da Yaki wajen shekarar 1807, ta wannan Kofar Sarakunan Habe suka bi suka fita suka gudu daga Katsina. Da farko sun fara zama Dankama daga nan Sai Damagaram, Wanda daga bisani suka koma Maradi da zama inda suka kafa Masarautar su, Mai suna Sarkin Katsina Maradi. Ance an ruguje wannan Kofar a Lokacin mulkin Dallazawa.
2. Kofar Sare. Ita Kofar Sare, ba tsohuwar Kofa bace kamar sauran Kofofin, Tarihi ya nuna lokacin Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo (1944-1981) aka sareta. Ance an yi ta tsakanin Kofar Guga da Kofar Yandaka, a dai dai inda Round about na KSTA yake yanzu. Mutanen gari ne suka sari Ganuwa suka rika bi suna wucewa, shiyyasa ake ce mata Kofar Sare.
3. Kofar Gazobi. Kofar Gazobi tsohuwar Kofa ce domin ta kafu tun lokacin da aka Gina Ganuwar Katsina wajen karni na 15. Ance ta wannan Kofar ne Gazobi yake bi yaje Karofi. Domin a lokacin Sarakunan Habe Gazobi Yana daya daga cikin manyan Hakimman Katsina, kamar yadda Dr. Yusuf Bala Usman ya bayyana acikin Transformation of Katsina. Ance an yita gefen Kofar Kwaya adai dai inda Sauki Fish yake yanzu.
4. Kofar Rafukka. Ta kafu tun lokacin Sarakunan Habe wajen karni na 15. Domin ta wannan Kofar ne Sarakunan Habe suke su shiga Rafukka domin aikin gona da noman Rani. Amma yanzu babu wannan Kofar.
Musa Gambo Kofar soro.