Saturday : January 11, 2025
05 : 13 : 21 AM

Zaɓen Kananan Hukumomi: Hon. Isah Miqdad AD Saude ya yanki Katin Zama Ɗan takara a Katsina.

top-news


Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times

Da Safiyar ranar Laraba 8 ga watan Mayu Mai taimakawa Gwamnan jihar Katsina na musamman akan Sabbin kafafen sadarwar zamani Hon. Isah Miqdad AD Saude ya isa Ofishin Jam'iyyar APC Shelkwatar dake Katsina don amsar katin shedar zama Dantakarar shugaban karamar hukumar Katsina a zaɓen da za a gabatar shekara mai kamawa ta 2025.

Honorable Isah Miqdad ya Isa Ofishin Jam'iyyar da misalin karfe sha daya saura mintina bisa rakiyar manyan mukaraban gwamnatin jihar Katsina daga karamar hukumar Katsina, inda ya amshi Katin daga jam'iyyar ta APC a karkashin jagoranci Shugaban jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Katsina Alhaji Mustapha Kofar Bai.

Daga cikin Jiga, jigan Jam'iyyar na karamar hukumar Katsina da su ka raka Dan takarar zuwa ofishin Jam'iyyar akwai Hon. Mannir Ayuba Sullubawa shugaban hukumar kula da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, Hon. Aminu Ibrahim Ida mai baiwa Gwamna shawara akan manyan ayyuka, Hon.Bishir Dan Gambo, Malam Gambo Runka Dan Agaji. Mai taimakawa gwamnan jihar Katsina akan harkokin Dalibai Hon. Nagaske da sauransu.