AN KAI KARAR KUNGIYAR KWALLO TA "KATSINA UNITED"DA NEMAN KUDI NAIRA MILYAN HAMSIN
- Katsina City News
- 07 May, 2024
- 421
.......anyi Kira a binciki yadda ake tafiyar da kulub din.
Mahmood Hassan
@ Katsina Times
Wani tsohon mai horas da "yan wasa na kungiyar kwallon kafa ta Katsina United mai suna Tony Tope Bolus, ya kai karar kungiyar kwallon kafar, a gaban hukumar kwallon kafa ta kasa "Nigeria football federation" akan yana neman hakkin sa na yarjejeniyar da sukayi da Katsina United , amma aka kore shi ba tare da wani laifi ba,ba kuma tare da bin ka'i da ba.
Koken yana kunshe a wata wasika da lauyan mai horas da yan wasan mai suna " W.O.ONATE and ASSOCIATES" ya rubuta a ranar 18/3/2024 sakataren hukumar NFF ya amshe ta a ranar 19/3/2024.
A wasikar wadda jaridun Katsina Times suka samu kwafi, lauyan ya bayyana yadda Wanda yake tsaya mawa aka dauke shi aiki a kungiyar wasan ta Katsina United a jadawali Goma sha takwas.
Wasikar ta bayyana a jadawali na sha bakwai da sha takwas cewa, Wanda suke tsaya mawa an kore shi ba tare da yayi wani laifi ba.ba kuma tare da bin ka 'i da ba.
Lauyan ya bukaci hukumar NFF, su sanya kungiyar kwallon kafa ta Katsina United su biya Wanda suke tsaya mawa naira milya Hamsin. 50,000,000.
Milyan talatin da takwas na kudin albashin sa ne da kuma alawus na yarjejeniyar shekaru biyu da akayi dashi Wanda baya da laifi aka kore shi kuma bai Saba wata ka 'i'da ba.
Milyan biyar na kudin lauya da ya dauka.sai kuma naira milyan bakwai na tayar masa da hankali da akayi.
A wata wasikar da jaridun Katsina Times suka samu, hukumar " Nigeria football federation "ta rubuta ma kungiyar kwallon kafa ta Katsina United a ranar 2 ga watan mayu 2024.
A wasikar NFF sun shaida ma Katsina United cewa an kawo koke akan su, kuma aka hada masu da takardar koken aka ce ana bukatar su bayar da amsa cikin kwanaki biyu.sannan ana bukatar su bayyana a ofishin NFF dake Abuja ranar 10/mayu/2024 domin su kare
kansu.
Jaridun Katsina Times, sun nemi jin ta bakin mai magana da muryar Katsina United, inda ya bayyana cewa bai da masaniya akan wadannan wasikun guda biyu da ake magana amma zai bincika.har zuwa rubuta rahoton nan bai Kira mu ba.
A wata sabuwa wata kungiyar mai zaman kanta wadda ake Kira da " concern citizen for sport development Katsina state " tayi Kira da abinciki yadda shugabannin riko na kungiyar kwallon kafa ta Katsina United ke gudanar da mulkin da kuma yadda suke tafiyar da harkokin kudi na kungiyar.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
All in All social media handles
07043777779 08057777762