Jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta kira taron gaggawa ga 'Ya'yan ta don Jaddada Aniyarsu ta shiga Takarar Zaɓen Kananan Hukumomi
- Katsina City News
- 06 May, 2024
- 432
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Katsina karkashin jagoranci Shugaban riko na jam'iyyar Hon. Musa A. Karim ta kira taron gaggawa na bayyanawa 'ya'yan jam'iyyar a fadin jihar Katsina cewa Takarar kananan hukumomi babu abinda aka fasa.
Mataimakin jam'iyyar PDP na riko a jihar Katsina Hon. Ibrahim Magaji Danɓachi a madadin shugaban na riko da bai samu halartar taron ba ne ya bayyana haka a babbar helkwatartar jam'iyyar a ranar Litinin.
Taron da Jam'iyyar ta kira ya kunshi dukkanin shugabannin jam'iyyar PDP na riko a matakin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina, inda sukai kira ga dukkanin 'ya'yan Jam'iyyar da ke sha'awar fitowa Takarar Kansila ko shugaban karamar hukuma, kofa bude take ana saida Fom na shiga Takarar kai tsaye a ofishin Jam'iyyar na jihar Katsina.
Hon. Magaji Danɓachi a madadin shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa, basa tare da wasu gungun mutane da suka ware kansu sukaiwa jam'iyya mai mulki aiki don kada sanata Yakubu Lado dan marke a zaɓen 2023.
Danɓachi ya ce su wadannan ba halastaccin 'ya'yan jam'iyya bane, suna ma jam'iyya Tuggu da zagon ƙasa ne, ne kuma kowa ya sani. Injishi.
Magaji Danɓachi yace Jam'iyyar PDP babu Lado Danmarke babu inda zata je, don babu mai iya rike ta sai lado, yace don haka su Lado Danmarke suke kuma shi suke bi shi ne Ruhin Jam'iyyar PDP a jihar Katsina.
A ranar Lahadi biyar ga watan Mayu na wannan shekara wani bangare na jam'iyyar PDP tsagin Dakta Mustapha Inuwa, Sanata Ibrahim Tsauri, Danmajalisar Tarayya Hon. Salisu Majigiri da Tsohon Sanatan shiyyar Daura, Sanata Ahamed Babba Kaita, da sauran su, suka kira taron manema labarai akan kin amincewa da kwamitin rikon kwarya da uwar jam'iyya ta ƙasa ta kafa.