An gudanar da Addu'o,i da Ƙaddamar da Littafin Marigayi Tsohon Shugaban Ƙasa a Katsina.
- Katsina City News
- 06 May, 2024
- 515
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Lahadi 5 ga watan Mayu 2024 ne tsohon shugaban Najeriya Marigayi Malam Umaru Musa Yar'adua ya cika shekaru goma sha hudu (14) da rasuwa, hakan ya sa Al'ummar jihar Katsina da kwamitin Tunawa da Malam Umaru Musa Yar'adua, a karkashin jagoranci Engr. Dakta Muttaqa Rabe Darma haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Katsina suka gudanar da wani gangamin taron addu'a a gidan gwamnatin jihar Katsina.
Taron Addu'o,in da aka fara gudanar da shi tun daga ranar Juma'a ta 3 ga watan Mayu, a masallatan juma'a na fadin jihar Katsina, a ranar Asabar kuma aka sadaukar da Abinci a gidajen marayu da marasa karfe da nufin Allah ya kai ladar ga makwancin tsohon shugaban Nijeriya Malam Umaru Musa Yar'adua.
A ranar Lahadi daidai da 5 ga watan Mayu yayi daidai da shekaru 14 da komawar malam Umaru Musa ga mahaliccin sa, an gudanar da Addu'o daga wasu manyan malamai a jihar Katsina, irinsu Babban Limamin Masallacin Juma'a na Katsina da ya samu wakilcin Sheikh Dayyabu Liman, da Sheikh Aminu Yammawa, Sheikh Badamasi Abbas, Sheikh Ismail bin Zakariyya Al'kashnawy, Sheikh Nazir Daura da sauransu.
Haka Zalika an gabatar da Muƙala akan shi kansa marigayin da irin kyawawan halinsa, tsarin Shugabancin sa tun a gida cikin iyalansa zuwa matakin gwamna da shugaban kasa da yanda yake da gudun duniya Kyakkyawar mu'amala da sauransu.
Farfesa Sani Abubakar Lugga shine Babban Bako mai gabatar da Kasida, inda ya gabatar da kasidar sa akan jagoranci/shugabanci da kuma iya mu'amala, inda ya bada misalin yanda shugaban ya kawo karshen takaddamar tsagerun Neja-dalta a cikin ruwan sanyi.
Lugga ya kara da cewa, da gwamnatin jihar Katsina zata bi irin salon da marigayin ya dauka na ganin kawo karshen takaddamar tsagerun Neja-dalta don kawo karshen rikicin masu satar mutane a jihar Katsina da yana da tabbas cewa za a samu saukin abin. A karshe yayi kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta jaraba.
Tsohon Gwamnan jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema ya gabatar da nasa jawabin a madadin Wadanda sukai aiki tare da marigayin da matarsa inda ya karanto wasu dabi'u da halayensa na gari, sana ya karanta sakonni na ta'aziyya daga Dandalin whatssApp na dukkanin ma'aikatan da sukai aiki tare da Marigayi Umar Musa Yar'adua tun a matakin gwamna zuwa Shugaban kasa.
Sanatan Katsina ta tsaki Malam Abdul'azizi Musa Yar'adua gabatar da wasu jawabai a madadin Iyalan Marigayin, gami da bayyana wasu maganganu masu sosa rai game da rasuwar tsohon shugaban Malam Umaru Musa Yar'adua.
Sarkin Daura Maimartaba Alhaji Faruq Umar Faruq ya bayyana irn alaƙarsa da Malam Umaru Musa, inda yace a duk duniya bashi da masoyi kamarsa, yace shine silar zamansa sarki.
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda Ph.D ya gabatar da Doguwar kasidar sa tun daga tushe akan rayuwar su da Malam Umaru Musa Yar'adua, yace tun a 1999 Horo da Tarbiyyar Malam Umaru Musa ce ke mulkin jihar Katsina a ko wane mataki tun daga gwamna zuwa majalisa da Sanata.
Manyan baki, 'Yan majalisu 'Yan Majalisar Zartaswar Kwamishinoni da sauran Mashawarta na gwamnatin jihar Katsina sun samu halartar taron addu'ar inda aka ƙaddamar da Babban Littafin da Engr. Muttaqa Rabe Darma ya wallafa akan rayuwar Marigayin da kuma wasu dabi'u da maganganu masu muhimmanci da zasu taimaki al'ummar jihar Katsina da Nijeriya baki daya.