Zaben Kananan hukumomi: "Bamu da wani zabi sai abinda Gwamna ya ce" -Jigajigan Jam'iyya APC a Mani.
- Katsina City News
- 02 May, 2024
- 454
Katsina Times
A ranar Talata 30 ga watan Afrilu me, Jigajigan Siyasa kuma 'Ya'yan Jam'iyya APC mai Mulki a jihar katsina daga karamar hukumar Mani, sun yi taron su na masu ruwa da tsaki akan zaben Kananan hukumomi da za a yi a jihar katsina, shekara mai kamawa ta 2025.
Taron da ya kumshi tattaunawa da fito da wasu al'amura akan zaben na Kananan hukumomi, Kuma a wajen taron da ya gudana a tsohon gidan gwamnatin jihar katsina, sun aje matsaya cewa, game da Dantakarar tasu da suke shirin tsaidawa na karamar hukumar Mani, sunce suna jiran umarnin maigirma gwamnan jihar katsina Malam Dikko Umar Radda.
A ranar juma'ar da ta gabata 26 ga watan Afrilu ne Honorable Shehu Kabir Jani, Mai mukamin Kula da Walwalar Al'umma na Jam'iyya APC ya Ayyana Aniyarsa ta tsayawa takarar karamar hukumar ta Mani a zabe Mai zuwa, a babban ofishin Jam'iyya APC na karamar hukumar, inda ya samu rakiyar Kansiloli 8 daga cikin 11 tare da sakataren karamar hukumar ta Mani.
Wadanda suka samu halartar taron na masu ruwa da tsaki sun hada da: Hon. Shafi'u Duwan (S.A), Alh. Mustapha Abdullahi Bujawa Babban Sakatare a ma'aikatar Fansho ta Kananan hukumomi, Alh. Garba Sanda Mani Shugaban Ma'aikatan jihar katsina, Rt. Hon. Aliyu Sabi'u Muduru Mai bawa Gwamna shawara akan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Alh. Hassan Yusuf Machika DAF a karamar hukumar Mai'adua, Injiniya Yakubu Tsagem (SSA to the Senate President), Hamisu Hassan Sakataren karamar hukumar Mani, Yusuf Haruna Bagiwa (Council leader) Sufyan Isyaku Shugaban Jam'iyya, Shehu Kabir Jani (APC Welfere Secretary), Abdulrahaman Danshehu, wakilan (Gwagware Contect and Mobilization Coordinator) Wakilin tsohon Danmajalisa Aminu Ashiru Mani (Hamza Bagiwa Sarkin Takardar Katsina), Shugaban (APC Support Engr. Sadiq Yusuf Machika) da sauransu.