MAI MARMATABA SARKIN KATSINA YA HALARCI TARON "NIGERIA HUNTER AND SECURITY SERVICE" NA WANNAN SHEKARAR.
- Katsina City News
- 01 May, 2024
- 612
Muazu Hassan
@ Katsina Times
Mai Martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini kabir Usman CFR ya halarci taron shekara na wuni daya akan matsalar tsaro a kasar nan da " Nigeria Hunters and forest security service " ta shirya a Abuja a ranar 31 ga watan afrilu 2024.
Taron Wanda ya gudana a dakin taro na "National centre for women development" Wanda ya samu halartar baki daga duk fadin kasar nan.da kuma Mai Martaba sarkin Katsina a matsayin Babban bako na musamman.
Mai Martaba sarkin Katsina ya samu wakilcin Alhaji Murtala Ibrahim safana ( Barden kerarriyar Katsina) a jawabin Alhaji Murtala safana a madadin Sarkin Katsina ya jinjinama wadanda suka shirya taron.ya kuma jinjina masu da suka samar da wani yanayi da za a tattauna matsalolin tsaro da kasar nan ke ciki, tsakanin wadanda abin ke shafa kai tsaye da tattauna yadda za a fuskance
Matsalar da maganinta.
Alhaji Murtala Ibrahim safana ya kara da cewa, duk miyagun dake ta addaci a kasar nan, kuma suka addabi mutane,daji shine mobayarsu, don haka, anan ne kungiyar ku ta shigo inda zata taimaka sosai.
Malam Murtala safana, ya kara da cewa kungiyar mafarauta ta hunters and forest security service tana da rawa da mai yawa da zata iya takawa wajen inganta tsaro a kasar nan daga ciki harda tattara bayanan sirri da fito da wani tsari, Wanda ba sai anyi amfani da jami "an tsaron kasa ba, wajen tunkarar wadannan miyagu dake cikin dazuzzukan mu
Barden kerarriyar Katsina, ya kara da Kira ga membobi da shugabannin (NHFSS) da su ci gaba da tafiya kafada da kafada da hukumomin gwamnati da Masarautun gargajiya domin samun hadin kai wajen yaki da matsalar tsaro a kasar nan.
Shugabannin (NHFSS) sun nuna godiyar su da jin dadin da halartar Mai Martaba sarkin Katsina,Wanda suka Misalta shi da sarkin al umma Wanda ya damu da halin da kasar sa ke a ciki.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
All in All social media handles