Tatsuniya (15); Labarin Wata Mata Mai Ya'ya Biyu
- Katsina City News
- 29 Apr, 2024
- 1008
Ga ta nan, gata nanku.
Akwai wata mata tana da 'ya'ya biyu, daya mace, daya kuma namiji. Macen ce babba, namijin kuma shi ne karami. Tana nan, tana nan sai wata rana ta kamu da rashin lafiya.
Tana cikin rashin lafiyar ta kira 'ya' yanta,
tana yi wa macen wasiyya cewa, ko da bayan ranta yaron ya ce zai yi wani abu to kada ta hana shi, ta bar shi. Bayan uwar ta rasu sai suka bar gidan, suka kama hanya suka nufi
wani gari daban.
Suna tafiya a cikin daji kwana da kwanaki, rannan sai wata babbar tsuntsuwa ta dauke su ta tashi sama da su, ta yi ta tafiya har suka isa daidai wani babban gari. Sai yaron ya dauki tsinke ya ce da yayarsa zai tsokale zumbutun tsuntsuwar, amma sai ta ce idan ya tsokale tsuntsuwar ai za ta yar da su.
Da ya ji haka sai ya ce mata ba uwarsu ta ce ta bar shi yayi duk abin da yake so ya yi ba?
Da yarsa ta ji haka sai ta yi shiru. Ya samo tsinke ya tsokali zumbutun tsuntsuwar nan. Ita kuwa sai ta zubar da su a wannan gai.
Can sai suka ga wani gida suka shiga, to ashe na wata tsohuwa ne. Da ta gan su sai ta yí maraba da su. ta ba su ruwa suka sha, ta tambaye Su daga Inda suke, sai suka kwashe labari suka ba ta.
Sai ta ce da su za ta Tiƙe su, amma kuma akwai wani dodo da yakan zo da dare yana cinye mutane kullum a garin.
Da dare ya yi aka kulle gida, sai yaron nan ya ce a ba shi karafa guda uku, wadanda zai yi amfani da su va soke dodon, kowa ya huta a garın. Da tsohuwa ta ji abin da yaro ya fada, sai ta ce da shi ba zai iya ba, amma sai ya dage a kan shi dai a ba shi. Tsohuwa ta yi masa yadda ya nema amma ba da son ranta ba.
Yaro ya hura wuta,ya zuba karafan a ciki. Da suka yi ja, sai ya ji wakar dodon yana cewa:
Wane ne ya isa ya ja da ni, a garin nan?
Wane ne ya isa ya ja da ni, ni dodo?"
Sai can yaron nan ya ce:
Ni ne na isa na ja da kai a garin nan.
Ni ne na isa na ja da kai,
Ni Auta, har ma na fi ka,"
Da dodo ya ji haka sai ya bude bakinsa ya yi wani irin karaji. Sai Dan'auta ya yi wuf, ya jefa masa karfe daya da ya yi jajir a cikin bakin. Sai
dodon ya cafe ya hadiye karfen, yaron ya jefa masa karfe na biyu, dodo ya cafe ya kara hadiyewa. Da yaron ya jefa masa na uku ya hadiye, sai dodon nan ya fadi rigija. Nan take ya mutu a kofar masallaci, ko shurawa bai yi ba.
Ganin haka sai Dan'auta ya bar takalminsa a wajen mushen dodo. Da asuba ladan ya je kofar masallaci domin ya shirya ya kira salla, amma sai ya ga mushen dodon nan shim. Sai ya je ya gaya wa Sarki abin da ya gani.
A cikin murna Sarki ya je ya ga mushen dodo, kuma ya tambaya ko wane ne ya kashe shi. domin an ga takalmin wanda ya kashe dodo, amma ba a san ko na wane ne ba.
Abu kamar wasa. sai Sarki va ce duk wanda ya sa takalmin nan ya yi masa daidai, to shi ne ya kashe dodon, kuma Sarki ya yi alkawari zai ba
wanda ya kashe dodon ladan rabin garin nan.
Masu kwadayin wannan kyauta suka vi ta zuwa suna gwada takalmi, anma bai zauna musu daidai ba Can sai aka ba Sarki labarin wata tsohuwa da ta yi baki, sai Sarki va sa aka kira ta ta sa takalmi bai yi mata daidai ba.
Daga karshe dai Dan'auta ya sa takalami, kuma ya yi masa daidai. Da dai aka tabbatar shi Dan'auta ne ya kashe dodo, sai Sarki ya cika
aIkawarin da ya yi. watau na ba shi rabin garin, Yaron kuwa ya karbi rabin gari ya ci gaba da mulki cikin nasara, shi da yayarsa.
Kurungus
Mun dauko wannan labarin daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman