Gidauniya Muqaddas Anas ta bada Gudummawar Kujerin Zama ga Makarantar Tarbiyyar Musulunci Mallakar "Markazul 'ilmu Wal'ibat a garin Katsina.
- Katsina City News
- 28 Apr, 2024
- 501
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Lahadi 28 ga watan Afrilu ne gidauniyar Muqaddas Anas ta gabatar da gudummawar kujerin zama ga tsohuwar makarantar nan mai suna "Tarbiyyar Musulunci, Mallakar Al'ilmu Wal'ibat" dake Sabon Layi wajen gidan Rediyon jihar Katsina.
Tun da Farko jagoran gidauniyar ta Mukaddas Anas Alhaji Yunusa Musawa ya gabatar da jawabi a takaice na Tarihin gidauniyar da Ayyukan ta da kuma abinda ta saka a gaba.
Yace "Muna bada Horo a matasa maza da mata akan koyarda sana'o,i don dogaro ga kai, han yasa mun yaye Daruruwan Mutane kuma a yakin yanzu sun dogara da kansu."
A jawabinsa, Musawa ya kara bayyana irin gudunmawar da cibiyar take bayarwa ga Addinin Musulunci da wasu cibiyoyin Musulunci a karkashin jagorancin Alhaji Muqaddas Anas.
Babban bako mai jawabi a wajen mika kyautukan kujerin ga Hukumar makarantar shine Liman Malam Abba Katsina, (Liman Abba). A jawabin da ya gabatar yayi godiya ga wannan cibiya, gami da karfafa gwiwa ga sauna Al'umma akan muhimmancin sadaukar da Dukiya don taimakon Al'umma.
A karshe liman ya karkare maganar sa da fatan Alheri ga shi wannan Dattijo da ya Assasa gidauniyar Muqaddas Anas gami da fatan Allah ya kara irinsu.
Shima a nasa jawabin shugaban gian Rediyon jihar Katsina Alhaji Lawal Attahiru Bakori ya yaba da wannan gidauniya da ya bayyana ta a matsayin gidauniyar Addini da ta bawa Addinin Musulunci muhimmanci, yace a madadin gidan rediyon jihar Katsina a shirye suke da bada gudunmawar da ta dace dari bisa dári.
An gudanar da Addu'o, i da Karatun Al'quranai mai girma a wajen Taron gami da zagaya ajujuwan makarantar don ganin kujerinda kuma takaitaccen bayani akan yanda tsaron koyarwar yake tun fiye da shekaru Ashirin da suka gabata.
Manyan Baki da suka halarci shedar mika kujerin sun hada da jagora kuma Shugaban gidauniya mr Alhaji Muqaddas Anas da Liman Abba, Dr. Mustapha Imam, Jagoran gidauniyar Muqaddas, Alh. Yunusa Musawa, Alh. Muhammad Isah Mani, Shugaban gidan rediyon jihar Katsina, wakilin Shugaban hukumar Zakkah da Waqafi, da ya wakilci babban Daraktan Hukumar. Da sauran baki.
Taron ya gudana a farfajiyar makarantar dake sabon layi da yammacin Lahadi.