YAKIN DA GWAMNA RADDA YAKE YI DA ’YAN FASHIN DAJI: RIBA, RADADI DA TARNAKIN DA KE CIKI

top-news

Daga Maiwada Dammallam

Duk da cewa har yanzu ba a kai ga tudun mun tsira ba, amma tabbas an yi abubuwa da yawa a cikin ’yan watannin da suka gabata don dawo da jihar Katsina kan turbar zaman lafiya da hayyacinta a sabuwar gwamnatin Gwamna Dikko Umar Radda, Ph.D. Sai dai za a iya fahimtar hakan ne idan aka yi kafada da kafada da girman matsalar rashin tsaron da Gwamna Radda da sauran gwamnonin yankin Arewa maso Yamma suka gada da kuma ba shakka, idan aka yi muhawara da wata manufa ta gaskiya ta fahimtar matsalar da samar da wani tsari na magance matsalar sau ɗaya kuma gaba ɗaya. Alhamdulillah, Gwamna Radda ya fito karara da sahihan dalilai da kuma sahihan manufa da ake bukata domin sauya mummunan labarin da ke ratsa jihar Katsina ko ma daukacin yankin Arewa maso Yamma.

Babu shakka, Gwamna Radda ya gaji jihar da aka riga aka yi wa kawanya, inda kananan hukumomi 23 suke karkashin ikon ’yan fashin daji. A haƙiƙa, yana sahun farko na wadanda illar munanan ayyukan ’yan fashin daji ya shafa, saboda bayan ya rasa ɗan'uwa ga kuma biyan kuɗin fansa don ceto wani dan’uwansa da ya fada komar ’yan fashin dajin. Shi ne wanda za a iya cewa ya isa gidan gwamnatin Katsina cikin zumudi da kuma fushi da mummunan halin da jihar Katsina ta shiga ciki shekaru da dama. Don haka ba abin mamaki ba ne da nan take ya kama hanyar kawo karshen matsalar cike da sanin ma'anar alkiblar da aka dosa, kuma mafi muhimmanci, ba tare da la'akari da rikitattun abubuwan da ke tattare da tsarin maido da zaman lafiyar da yake tunani ba. Wani abu da ke ƙara nauyin matsalar nan ita ce budaddun kan iyakokin kasashen waje da ke jihar wadanda suke taimakawa wajen kwararar kanana da ma manyan makamai waɗanda Gwamnatin Tarayya ta yi kamar ba ta da wani tasiri don rage tabarbarewar al'amuran. Hakan bai buge wa Gwamna Radda gwiwa ba, ya ma kara zaburar da burinsa na kawo sauyi ne. Alhamdu lillahi, azamarsa tana biyan kudin sabulu.

Babu shakka lokacin da Gwamna Radda ya hau kan mulki, shekaru da dama da aka shafe ana fama da matsalar rashin tsaro ya kawar da wani kaso mai tsoka na 'yan jihar daga hanyoyin samun rayuwa da ma mutunci, tare da mai da da yawan su ko dai 'yan gudun hijira ko kuma masu kwana a kan titunan manyan garuruwan jihar. Wannan, sai kuma ya haifar da wata sabuwar matsala mara kyau ta rashin aikin yi, wanda ya samar da babbar runduna wacce za ta iya zama ta 'yan fashi ko na masu aikata sauran laifuka daban-daban. Sai kuma tsarin shari’a ya gaza wajen jaddadawa a zukatan 'yan jihar cewa aikata laifuka ba ya da riba. A taƙaice, haɗuwa ce ta al’amura da yawa suka kai mu inda muke a yau. Wannan duk ya haɗa da sanya batun rashin tsaro ya zama matsala mai wuyar warwarewa; wanda ke buƙatar fiye da nazarin ’yan "Tik-Tok" da masu rubutun ra'ayi a yanar gizon da suka horar da kansu don fadakarwa da samun sanayya ta jama'a, don warware matsalar ko ma fahimtar ta kawai.

Don fita daga cikin wannan rudami, to dole ne mu yi la'akari da duk al’amuran da ke tattare da matsalar yayin da muke neman daidaita batun rashin tsaron yadda ya kamata. Dole ne kuma mu ware ka'idodin rashin tsaro, da tsarin tsaro namu da abubuwan haɗin gwiwa, na zahiri da kuma gaskiyar da ke jagorantar muhawararsu. A koyaushe ina jayayyar cewa tsaro yanki ɗaya ne wanda dole ne mutum ya kasance yana da ba kawai masaniyar tushen buƙatun ba, amma mafi kyawun bayanai don fahimta ko yin muhawara cikin hikima. Misali, an yi amannar - a zahiri magana ce ta tsarin mulki - cewa gwamnati ce ke da alhakin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa. Duk da haka, mutane kaɗan ne kawai za su iya faɗi daidai ko wace “gwamnati” ke da wannan alhakin ko kuma yadda kariyar wannan magana ta tsarin mulki take. Bacin haka nan, ko dai da gangan ko kuma bisa jahilci, mutane kalilan ne za su iya nuna cikas din da ke rage wannan magana ta tsarin mulki zuwa wata ka'idar tsarin mulkin da ba ta da amfani da aka mai da ta tamkar gaskiya.

Don a fayyace komai kuma ba tare da wani taraddudi ba, Gwamnatin Tarayya ce ke da alhakin kare rayuka da dukiyoyi, akalla. Ita take da hakki na musamman na tashe-tashen hankula wanda ba ta rabawa da wata gwamnati a kowane mataki. Ita ce mai kula da dukkan hukumomin tsaro da duk wata cibiya mai alaka da hakan. A nan ne rudun ya faro kamar yadda, a daya bangaren kuma, kundin tsarin mulkin da ya mamaye duk wani batun tashe-tashen hankula na jihohi da kuma mai da kare rayuka da dukiyoyi a hannun gwamnatin Tarayya, sai kuma ko ta yaya ya juya, ya mayar da gwamnonin jihohin “Manyan Jami’an Tsaro” na jihohinsu, ba tare da wani hakki na murkushe tashin hankali ko iko a kan hukumomin tsaro ba – tamkar dai aika su cikin fagen fama ido rufe tare da daure hannayensu biyu ta bayansu. Hikimar da ke tattare da wannan sabani shi ne cikakkiyar maudu'i na wata rana.

Ita kanta Gwamnatin Tarayya tana fama da illar ra’ayin da ke cewa ita ke da alhakin kare rayuka da dukiyoyin ’yan Nijeriya, sai dai idan ta kowace hanya za ta iya yin ma’ana ga Gwamnatin Tarayya ta yi wa kasa mai mutane sama da miliyan 200 tsaro yadda ya kamata, duk da yawan jami’an tsaronta in sun hada karfi da karfe yawansu kusan miliyan 3 ne a dukkan hukumomin tsaro - shi ma wani batu ne na wata rana.

Idan aka tsaya kan jihar Katsina kawai, Gwamna Radda bai bar kowa a cikin shakku ba game da aniyarsa da kudurinsa na yin amfani da dukkan karfin ikonsa (ko da na kashin kai ne inda ya dace) wajen dawo da zaman lafiya a jihar Katsina. Ya yi alkawarin kashe duk wani kwabo a cikin baitul mali, idan har abin da ake bukata ke nan don samar da zaman lafiya a jihar, ga kuma zuba jarin biliyoyin Naira a fannin tsaro don inganta ayyukan jami’an tsaro, wanda babu shakka ana ganin hakarsa na cimma ruwa. Sayen karin sabbin motocin yaki guda 10 samfurin APC, bayan kashe sama da Naira Biliyan 7 da ba a taba ganin irinsa ba domin tsaro da kuma kafa rundunar tsaron jihar mai suna Katsina Community Watch Corp (CWC), duk hakan na nuni ne da yadda Gwamna Radda ya kuduri aniyar sauya yanayin tsaro a jihar, duk da bayyananniyar tarnaki na siyasa, kudi da ma kundin tsarin mulki.

Duk da wannan abin yabawa ne, ya kamata mu dauka cewa tafiyar ba mai sauki ba ce, don haka, dole ne kowa ya tashi tsaye wajen mara wa Gwamna Radda baya wajen ganin an dawo da zaman lafiya a Jihar Katsina ba tare da duban wata maslaha ba sai ta jihar da yankin Arewa maso Yamma gaba daya. Babu wata damar yin sassauci ko sakwa-sakwa a wannan al’amari na tsaro. Sa'an nan kuma, dole ne a yi la'akari da irin sarkakiyar yakin da yanayin siyasarmu a yayin da ake yin muhawara kan nasarar da gwamnatin Radda ta samu kan wannan lamari. Tabbas, babu wanda zai musun cewa a halin yanzu jihar Katsina na ci gaba da samun wasu hare-hare a wurare masu rauni a yankunan da babu cikakken tsaro. Ya kamata a yi tsammanin hakan. Kamar cin hanci da rashawa, fashin daji ba zai mutu a kwance ba. Ma'aikatan da aka gajiyar da su da karancin kudade wani bangare ne na matsalar da 'yan fashin daji za su yi amfani da su a dabi'ance don kiyaye kasancewarsu a cikin tsarin ta da hankula a cikin zukatan 'yan kasa.

Hare-hare a kan wurare masu rauni daga ‘yan fashin daji dabara ce mai sauki daga ‘yan fashin don ci gaba da rataya ga mafi kankantar kayan aiki a cikin makamansu - TSORO! 'Yan fashin daji da masu tayar da kayar baya sun fi samun nasara ta hanyar sanya tsoro a zukatan 'yan kasa. Wannan ne dalilin da ya sa 'yan fashin dajin ke yin rikodin da kuma sakin bidiyo na munanan ayyukansu ga jama'a. Suna da nufin cusa burgewa a cikin zukatan ‘yan ƙasa na ikon yin tashin hankali da suke ganin suke da shi da kuma ci gaba da sanyaya gwiwar jama'a. ’Yan fashin daji ba sa fitar da bidiyo don nuna cewa su jarumai ne, shi ya sa suke sanya abin rufe fuska a cikin bidiyonsu don boye hakikaninsu. Suna yi ne kawai don tsoratarwa da danne jama'a ta hanyar da a hakikani tana nuna su matsorata ne ma.

Kuma a nan ne dukkan mu ke da babbar rawar da za mu taka. Hanya mai ban tsoro da muke yada al'amuran rashin tsaro - wani lokacin ma ta amfani da tsofaffi ko bidiyoyin da ba a tantance ba - tabbas wani cikas ne ga kokarin gwamnati na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ba don manufar murkushe fadakar da jama'a ba ne ya kamata a yi taka-tsantsan wajen ba da rahotannin abubuwan da suka faru na rashin tsaro da kuma muhimmantar da abubuwan da suka shafi tsaro sosai, wanda ba da rahoton su yana buƙatar mafi girman nauyi da taka- tsantsan. A cikin himmarmu na ba da rahoton al'amuran rashin tsaro, galibi muna yin barna fiye da kyautata tunanin gamayya da gwamnati don kiyaye al'umma. Yawanci mukan karke ne da zuzuta ayyukan masu aikata muggan laifuka da kuma nuna su kamar sun fi karfin  doka kuma da alama ba za a iya sarrafa su ba, don haka, sai ya zama ana saita tunanin jama'a da kuma hana gwamnati jajircewar 'yan ƙasa don shiga cikin abin da ya kamata ya zama aikin haɗin gwiwa tsakanin 'yan ƙasa da gwamnati don kare rayuka da dukiyoyi.

Ba tare da fargabar samun sabani ba, bari in sake cewa, babu wata gwamnati da ke da karfi ko wadatar da za ta iya tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi ta hanyar gurbatacciyar ma’anar da muka fahimci bangaren kundin tsarin mulkin Najeriya da ya tilasta wa ‘yan Nijeriya amincewa da cewa samar da tsaro ga al’umma abu ne da za a iya yi. Haka nan, babu wata gwamnati da ta isa ta yi shi ita kadai.

'Yan adawa ma ba sa taimakawa al'amura. Abin takaici ne kawai yadda wasu mutane ke raina al'amuran tsaro don kawai su soki gwamnati su ci maki mai arha na siyasa. Waɗannan maki na iya zama mai arha amma suna da mutuƙar hatsari kuma suna iya cinye mu duka. Halin da ‘yan adawa ke nunawa na ganin duk wani hari da ‘yan bindiga za su kai wa ‘yan kasa a matsayin gazawar gwamnati tukuna, ba tare da yin la’akari da al'amuran da na ambata a baya ba, amma kawai don samun maki na siyasa mai arha yana da matukar tayar da hankali. Ba wani abu mai wuya ba ne fahimtar cewa 'yan fashin daji ba masu mutunta alaƙar jam'iyya ba ne, kuma duk muna cikin wannan matsalar tare, kuma tabbas za mu iya yin iyo ko nutsewa tare a ciki.

Ba daidai ba ne, don haka, a ɗauka cewa bai wa gwamnati goyon baya da haɗin kai don yakar 'yan fashin daji da sauran matsalolin zamantakewa, tamkar yi wa gwamnati wani alheri ne. Nesa da hakan, nuna goyon bayanmu da haɗin gwiwarmu a wannan fanni, aiki ne na al'umma, wanda yin sakaci da shi zai iya haifar da mummunan sakamako. DOLE DUKKAN hannaye su kasance a kan teburi don yaƙi da barazanar a tare. Wannan shine ainihin ma'anar TAIMAKON KAI. Kada mu ƙyale siyasar bambance-bambancen jam’iyya ta ɓata tunaninmu na aminci ko kishin ƙasa. Gaskiya ne cewa gwamnati ba za ta iya yin aikin ita kadai ba. Tana yaƙi da rundunar masu laifi ne waɗanda za su iya kai hari ga jama'a a cikin minti ɗaya, sannan a cikin minti na gaba, su narke, su cuɗanya da jama'a, kawai don su nuna su cutarwar ta shafa. Wani abu da ya yi kama da gaba kura baya siyaki.

Wannan ya haifar da wata muhimmiyar tambaya ta rashin amana da rashin mutuntawa da ake ganin ita ce tushen dangantakar da ke tsakanin wasu 'yan ƙasa da gwamnati, galibi ta hanyar dalilan siyasa. Ya zama ruwan dare karantawa ko kallon sharhi da bidiyoyi na ban dariya da nufin “fadakarwa” ga al’umma kan ayyukan gwamnati, duk da haka cike yake da shaci-fadi ko ma kage-kage da aka kera don yi wa Gwamna da gwamnati ba’a ta hanyar tozarci. Me ya sa, alal misali, zai zama matsala idan gwamna ya bar  jihar Katsina ya tsallake teku don gina hanyoyin sadarwar da za su jawo wa al’ummar Jihar Katsina dimbin alfanu? Kai, wai ma wa ya ce raya jiha yana da sauki? "Ai da ma gwargwadon kudinka, gwargwadon shagalinka."

Wani kyakkyawan misali a nan shi ne ziyarar Gwamna Radda da ke gudana a birnin Washington DC na Amurka, tare da wasu gwamnoni 10 daga yankin Arewa maso Yamma da ake ta muhawara kamar tafiya hutun Disneyland, alhali gwamnonin sun yi tafiya zuwa Majalisar Dinkin Duniya (UN) ne don amfani da wasu hanyoyi, da haɗa kai da Majalisar Dinkin Duniya tare da jawo hankalinta sosai game da ta'addancin da ke faruwa a Arewa maso Yamma, wanda da alama ya bijire wa duk wata mafita ta cikin gida. Kuma ba kamar gwamnonin nan sun sudade sun fice daga Najeriya ba ne. ‘Yan Najeriya sun samu cikakken bayani game da manufofinsu da kuma muhimmancin ziyarar tasu ga jihohinsu, duk da haka, ba mu da matsala muna kallon yadda wasu ke sanya mutuncinsu da sadaukarwarsu a kan layi kawai saboda sun amsa kiran yin hidima ga al'umma.

Kari cikin alfanun ziyarar wadannan gwamnonin ga Majalisar Dinkin Duniya shi ne, hakan zai ba su damar tattauna yadda za a magance matsalolin rashin tsaro da ke da nasaba da kasashen duniya kamar kwararar kananan makamai da manyan makamai da ake jibgewa a Afirka, galibi daga Turai, Asiya da sauransu. Kuma za ta ba su damar samun kudade da ƙwarewa da haɗin gwiwa tare da abokan hulɗa na kasa da kasa don musayar bayanan sirri, shirye-shiryen horar da jami'an tsaro na gida, har ma da bincikar damar samun taimakon kuɗi da aka sadaukar don yaki da 'yan fashin daji. Bugu da kari, ziyarar za ta taimaka musu wajen kulla alaka da masu ruwa da tsaki na kasa da kasa, wadanda suka hada da hukumomin tsaro, kungiyoyi masu zaman kansu, da kamfanoni masu zaman kansu masu albarkatu da kwarewar da suka shafi yaki da ‘yan fashin daji. Don haka, wanne daga cikin waɗannan fa'idodin ne bai dace da a kashe kuɗi don cimmawa ba? Yin suka yana da matukar muhimmanci a tsarin dimokuradiyya, amma dole ne ya kasance mai kaifin hankali da aka yi da ingantaccen rubutu tare da kyakkyawar niyya, ba tare da wani son rai ba, sai na taimakon al'umma. Kada ta hanyar wautar mu, mu jefar da jariri da ruwan wankan.

Maiwada Dammallam shi ne Babban Daraktan Yada Labarai na Gwamna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *