Iyalan Marigayi Alhaji Danlami Sun Maka Gwamnatin Kaduna A Kotu Bisa Rushe Musu Muhalli
- Katsina City News
- 27 Apr, 2024
- 397
Kotu ta sanya ranar yanke hukunci
Daga Zailani Mustapha
Iyalan Marigayi Alhaji Hamid Danlami sun maka gwamnatin jihar Kaduna, hukumar tsara birane ta jihar, KASUPDA da kuma Kwamishinan shari’a kuma Babban mai shari’a na jihar, wato a kotu bisa rushe musu muhalli ba bisa ka’ida ba tare da take musu hakkinsu na mallakar muhalli, inda suka nemi kotu da ta bi musu hakkinsu.
Shari’ar mai taken; ‘Dr. Ibrahim Abdulhamid Danlami Vs Kaduna State government & 2 others’ ranar 6 ga watan Maris din 2024, ta kasance ranar farko ta soma sauraren shari’ar sai dai mai shari’a Kabir Dabo da lauyoyin gwamnati da na Kwamishinan shari’a da na KASUPDA ba su samu damar halartar kotun ba wanda ya sanya aka dage shari’ar.
Shari’ar dai na gudana ne a babban kotu jiha dake Zariya a karkashin mai shari’a Alkali Kabir Dabo.
Zaman shari’ar na farko wanda bai samu halartar gwamnatin jiha, Antoni janar, da KASUPDA ba, da kuma Alkali ya sanya kotu ta dage karar domin a sake aikawa da wadanda ake kara takardar halartar kotun. Inda aka dage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Afrilun 2024 domin soma sauraren karar.
A zaman shari’ar da aka yi a ranar Laraba 24 ga watan Afrilun 2024, wakilan gwamnati da na Antoni da kuma na KASUPDA ba su samu halartar kotun ba, sai dai sun rubuto cewa suna son a sanya watarana domin su halarta.
Barista Haruna Magashi da Barista Ishak sune lauyoyin wadanda suka shigar da kara, sun nemi da Alkali da ya saurari shari’ar duk da rashin halartar lauyoyin gwamnati da na KASUPDA da Kwamishinan shari’a, domin a cewarsu dukkaninsu sun san da shari’ar, Alkalin ya karbi korafinsu inda ya saurari karar da suka shigar gabansa.
Bayan sauraren dukkanin korafe-korafe, kotun ta sanya ranar 23 ga watan Mayun 2024 a matsayin ranar yanke hukunci.
Da wakilinmu ya tuntubi Barista Yushau bn Shaikh, jagoran lauyoyin da suka shigar da karan ya tabbatar mana da cewa; shari’ar an sanya ranar yan