Amurka Ta Ba Mu Bayanan Sirrin Tsaron Arewacin Najeriya
- Katsina City News
- 26 Apr, 2024
- 545
Gwamnonin sun ce sun samu bayanan sirrin tsaron jihohinsu a Amurkar fiye da yadda suke samu a Najariya, "Wani bayanin ma sai ka yi mamakin yadda suka same shi."
A tattaunawar da ya yi da BBC gwamnan jihar Katsina Mallam Dikko Ummaru Radda ya ce sun samu dabarun hanyoyin da za su shawo kan matsalar tsaron da ke addabar jihohinsu.
Gwamnan ya ce sun ƙaru da dabaru da shawarwarin da za su yi masu amfani wajen shawo kan matsalar tsaron jihohinsu, " Mun kuma gaya masu damuwarmu da abin da muke tsammani daga Amurka."
Ya ce idan har gwamnatin Amurka cikin ƙanƙanin lokaci za ta kuɓutar da wani ɗan ƙasarta da aka taɓa sacewa a Nijar aka shiga da shi arewacin Najeriya, "Idan Amurka na da wadannan dabaru me zai hana ta taimaka mana da su da fasahohi da za mu yi amfani da su."
Mallam Dikko ya ce taron kuma ya duba bangaren tattalin arziki domin magance matsalar talauci cikin al'umma, inda ya ce hakan zai taimaka wajen magance matsalar tsaro kwarai: " Akwai dabaru da dama da muka kalla wanda in sha Allah idan muka koma Najeriya za mu fara ƙaddamar da su."
Gwamnan ya ce sun tattauna da hukumomi da masana'antu da masu sanya hannun jari, a kan yadda za su inganta masu harkar noma da harkar wutar lantarki tare da taimaka wa gwamnatoci wajen haƙo ma'adanai da ke akwai a Najeriya wadanda za su taimaka wajen habaka tattalin arziƙin arewacin Najeriya.
Gwamnan ya ce sun samo hanyar da za ta taimaka masu wajen fitar da yankin arewacin Najeriya daga cikin matsalar rashin ilimi da talauci da rashin zaman lafiya da muke fama da su.
Dikko Radda ya ce ba za su ba kansu wani wa'adi na kawo ƙarshen matsalar ba saboda magance matsalar na daukar lokaci, Inda ya ƙara da cewa dalilin da ya sa suka je Amurkar saboda ba za su samu wasu bayanan ba sai sun yi mu'amala da wasu ƙasashen.
Gwamna Radda ya ce sun tattauna da ƴan majalisar dokokin Amurkar kan matakan da suke dauka da ke kawo cikas ga yaƙin da ƙasashen Afirka suke yi da ta'addanci.
Jihar Katsina dai na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro musamman ta ‘yan fashin daji wadanda ke kai hare-hare garuruwa da kauyukan jihar baya ga satar mutane don neman kudin fansa da kuma sace dukiyoyin mazauna yankin.