Shehu Kabir Jani Ya gabatar da kansa a matsayin Dantakarar Shugaban karamar hukumar Mani.
- Katsina City News
- 26 Apr, 2024
- 496
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Shehu Kabir Jani daga Jam'iyya APC mai Mulki ya bayyana Aniyarsa ta tsayawa Takarar Shugaban karamar hukumar Mani a jihar Katsina a ranar juma'a tare da Dimbin magoya bayansa da suka rakashi ofishin Jam'iyyar domin gabatar da kai a hukumance.
Jani bisa rakiya tare da goyon bayan Kansiloli Takwas daga cikin goma sha daya da karamar hukumar ke da su, da Sakataren karamar hukumar ta Mani mai ci, Tsaffin 'Yan Takara da suka taba neman shugabancin duk sun mara masa baya zuwa Babban Ofishin Jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Mani a ranar juma'a 26 ga watan Maris, don mika takardar sa ga Uwar Jam'iyyar ta APC.
A tattaunar sa da jaridun Katsina Times, sakataren ƙaramar hukumar kuma tsohon Dantakarar karamar hukumar ya bayyana cew su da ke neman takara sun yanke hukuncin marawa Honorabul Shehu Kabir baya a zaben kananan hukumomi da za a gudanar a shekara mai kamawa, yace domin saukaka ma uwar jam'iyya da kuma nuna hadin kai kasantuwar dukkanin su 'ya'yan Jam'iyyar ne uwa daya uba daya.
Da yake gabatar da jawabin sa, Dantakarar shugaban karamar hukumar ta Mani, Honorable Shehu Kabir Jani ya bayyana dalilan sa na fitowa Takara. Inda yace ya amsa kiraye-kirayen Al'umma ne, don haka ya share masu hawayensu.
Jani yace, dama Siyasa a cikinta muke munsan matsalolin 'Yan karamar hukumar Mani don haka insha Allah, zamu yi iya kokari ganin mun magance su." Injishi
Honorable Shehu Kabir Jani shine shugaban walwala da jin dadi na jam'iyyar APC, kuma yana cikin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta APC.
Magoya baya 'yan uwa da Abokai ne sukai dafifi wajen raka Honorable jani inda ya samu kyakkyawar tarba daga shugabannin jam'iyyar ta karamar hukumar Mani.