APC Za Ta Lashe Zaben Gwamnan Kogi Da Kaso 99 – Ganduje

top-news

Culled From Aminiya 

Ya ce suna da kwarin gwiwar jam'iyyarsu ce za ta lashe zaben

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce yana da kwarin gwiwa jam’iyyarsa za ta lashe zaben Gwamnan Jihar Kogi na watan Nuwamba da kaso 99 cikin 100 na kuri’un da za a kada.

Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin kaddamar da kwamitocin yakin neman zaben jam’iyyar a matakin jihar da na kasa.
Za a gudanar da zaben ne ranar 11 ga watan Nuwamba mai zuwa.

A cewar Ganduje, “Kun dandana shugabanci na gari a hannun Yahaya Bello, muna fatan ku samu fiye da haka idan kuka zabi dan takararmu, Alhaji Usman Ododo.

“Ba ma tsammanin kuri’ar da za ku ba mu ta gaza kaso 99 cikin 100 a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba mai zuwa a Jihar Kogi,” in ji Ganduje.

Shugaban jam’iyyar ya kuma ba ’yan Jihar ta Kogi tabbacin cewa Shugaban Kasa Bola Tinubu zai tabbatar da samar da yanayi mai kyau da zai sa a yi sahihin zabe kuma cikin lumana a Jihar.

Tsohon Gwamnan na Kano ya kuma ce, “Yana da muhimmanci a lura cewa mun fito da nagartattun tsare-tsare wajen ganin jam’iyyarmu tana da tsari tun daga tushe, ta hanyar bude ofisoshi a dukkan mazabu 8,813 da ke fadin Najeriya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *