Ko Kunsan Abubuwan Da Suke Faruwa a Jami'o'in Ƙasar Amruka Yanzu Haka Kuwa?
- Katsina City News
- 25 Apr, 2024
- 454
Daga Bilya Hamza Dass
Yau kwana 7 a jere ɗalibai sun hana karatu a manyan jami'o'i 21 da suke garuruwan Amruka daban-daban da suka haɗa da Colombia, New York, Textas, Miami California da sauran su saboda zargin Amurka da hannu dumu-dumu a k*san kiyashin da ake yiwa mutane a Gaza! Lamarin ya fara daga makarantar Columbian University da take New York, wacce ake kira da SP-Elite University, inda daga nan ne ake yaye mafi yawan manyan ƙasar da ƴan siyasa da jagororin Amruka. An fara da ɗalibai 72 mafi yawan su Mata ne, inda suka kafa tanti dayawa suka ce zasuyi zaman dirshan na tsawon awa 24 har sai gwamantin Amurka ta dakatar da bada tallafin makamai ga Isra'ila da suke amfani da shi wajan wanan aiki!
Kafin cikar awa 24 sai da adadin daliban ya kai 216, nan take sai shugabar makarantar ta sanya ƴan sandan NYPD suka kama wasu daga masu zanga-zangar mutum 108, kama dalibai da akayi shi ne ya sanya sauran ɗalibai sukace basu yarda ba inda suma suka shiga jerin masu kiran da fara zanga-zangar. Bayan kwana 2 da farawa adadin daliban ya kai 800+ wanda haka na nufin rabin dalibai da suke karatu a makarantar sun shiga kenan. Ƴan sanda sun cigaba da kama ɗaliban da suke cigaba da zama wajan har zuwa kwana 4.
Ranar da aka cika kwana 4, Jami'ar ta aika sako ta email ga dalibai 55 cewa ta dakatar da su har na tsawon shekara 1, saboda shiga zanga-zangar, sannan kuma tayi umurni ga ƴansanda suyi gagarumin kamu da suka kira da ‘Mass Arrest’ wanda suka kama mutu 361 aka kaisu gidan yari. Faruwan hakan shi ne ya tanfatsa lamari ya shiga wasu jami'o'i wanda a rana ta 5 sai da jami'o'i manya guda 13 sukayi boren shiga aji suka dakatar da komai suna kira da basu yarda a dinga kwasan harajin su ana aikawa Isra'ila ba!. Dayawan Malamai daga jami'o'in suma sunbi sahu suna kiran a tsaida kisan kiyashin. An jiyo Firaministan Isra'ila Benjamen Natanyaho yana faɗin cewa, abinda ke faruwa a Jami'o'in Ƙasar Amruka abin baƙin ciki ne.
Yanzu haka ɗaya daga cikin manyan jami'ar ƙasar Harvard ta shiga jeri. Yau an shiga kwana na 7 kenan, ɗalibai sunki yarda. Wata daliba da tace ta samu email kan dakatar da ita, tace ko da gidan yari aka kaita ta dawo zata cigaba. Ɗaliban suna cigaba da samun yabo da goyon baya daga sassa daban-daban na duniya. Manyan mutane a Amruka irin su Johson Jirrry, da shugaba Majilisar wakilai da Dattawa sun halarci wajan suna kiran daliban su koma aji amma sun sha ihu. Ɗaliban sunce babu gudu babu Ja da baya. Zan sanya wasu bidiyon yanda abun ke faruwa a comment section.