An Kama Sojojin Gona da Sunan Hukumar Hisbah a Katsina.
- Katsina City News
- 23 Apr, 2024
- 677
An Kama masu shigar Sojan Gona da Sunan Hukumar Hisbah a Katsina.
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Hukumar Hisbah a jihar Katsina ta Cafke Sujojin gona da sunan Hisbah suna karɓar na Goro a gidajen Baɗala.
A ranar Litinin 22 ga watan Afrilu Hukumar Hisbah a Katsina ta cafke wasu Matasa biyu Sha'aibu Mamman Ifo, da Aliyu Umar Liman bisa zargin Sojan gona da sunan Hisbah.
Matasan biyu da suka amsa laifinsu a gaban wakilan Jaridar Katsina Times sun bayyana yanda suka tsara takarda dauke da sunan hukumar Hisbah, tare da sunayen gidajen Ɓadala a jihar Katsina wadanda suke bi daya bayan daya suna amsar cin hanci a wajen su.
Sha'aibu daya daga cikin wadanda ake zargi da sojan gona, yace ya shiga wannan rashin kyautawar ta dalilin abokinsa da yake Mataimaki ne na Musamman wato SSA ga Hukumar Tsaftace Muhalli ta SEPA.
Yace "shine yazo ya jani, gami da sharrin zuciya har muka aikata wannan kuskuren, da nake kira ga Matasa akan kada su biye wa son zuciya irin yanda mukai, lallai munyi kuskure."
Aliyu Jikan Liman na biyu da ake zargi ya bayyana yanda Sha'aibu Mamman ya bashi shawarar su dunga aikata Sojan gona da Sunan Hisbah, kuma ya biye masa, wanda yace sunje wajen Caca, har wuri biyu sun amshi na goro (Cin hanci) kuma sun yi List na gidajen Ɓadala a Katsina da nufin su dunga kai masu ziyarar amsar dan abinda ya samu don su soke sunansu daga wadanda za a kaiwa samame.
Da yake Tattaunawa da Katsina Times, Malam Nafi'u M. Aƙil Jami'in Hurɗa da Jama'a na Hukumar ta Hisbah ya bayyana yanda suka samu bayanan sirri na Matasan biyu da yace basu da Alaƙa da Hisbah ta kusa ko ta nesa, yace "Basu taɓa Hisbah ba basu taɓa sa kakin Hisbah ba, sun aikata son zuciyar su ne kuma Allah ya tona musu Asiri." Inji shi.
Malam Nafi'u yace Hukumar Hisbah bata san da su ba kuma ta kamasu ta tabbatar da laifinsu don haka ta miƙasu gaban Ƙuliaya domin su girbi abinda suka aikta.
"Hukumar Hisbah tana Aiki bisa gaskiya kuma bata Amsar duk wani Kudi da sunan cin hanci, balle ma abinda ya shafi hana Mummuna da Umarni da Kyakkyawa wanda kuma wannan Umarnin Allah ne". Inji shi.
Gyara: A sakin Layi na karshe Mun cire shi, sakamakon Cece-kuce da ya haifar.
Muna fata za'a dauki Bidiyon da muka saki na masu laifin da ake zargi a matsayin Hujja.
"Mun samu Tattaunawa da Babban Mai Taimakawa Gwamnan jihar Katsina akan Sabbin Kafafen yada labarai na Zamani". Muna kuma kira ga duk wanda yaga rubutun ko ya dauka sai yayi la'akari da gyaran da mukai.
Da fatan za'a bibiyi bidiyon da kyau mun gode.