Tatsuniya; (11) Labarin Kurege da Kura na 2
- Katsina City News
- 22 Apr, 2024
- 529
Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana Kurege da Kura suna yawo, sai suka tsinci kyallen fatarí. Sai Kurege ya ce, bari ya je ya dinka musu riguna da shi.
Ya je ya dinko riguna biyu, amma girmansu daya. Ya bai wa Kura đaya. Da Kura ta saka sai rigar ta matse ta, ta shake mata wuya saboda ta yi mata kadan.
Sai Kurege ya ce da Kura tun da rigar nan ta yi mata kadan., sai ta bar masa ita. Da Kura ta ji haka sai ta ce masa: Da man ka cuce ni ne tun da ka dinka rigata daidai da taka, sai ka dauka."
Kurege ya hada duka biyun, suka shiga jeji don su farauto abin da za su ci.
Da suka kamo namun daji da yawa sai suka dawo gindin wata bishiya, suna hutawa. Kurege yana so ya cinye naman shi kadai, amma ya rasa yadda zai yi. Can sai ya hango wasu 'yan mata a bakin rafi, sai ya dubi Kura ya ce: "Ga yan mata can, mu je mu yi musu magana.
Sai Kura ta yarda, suka je suka tarar da 'yan matan suna hira. Suka zauna suna sauraron hirar. Da Kurege ya ga hira ta fara yin dadi sai ya ce da Kura su íe su dafa naman nasu. Sai Kura ta ce ita tana nan a wurin hira,
ba za ta je ba.
Shi kuwa Kurege sai ya je domin ya dafa musu naman. Ashe ya sami abin da yake so, wato sai ya zabi nama mai kyau ya zuba a jakarsa, ya boye.
Sai ya samo naman mushe ya dafa, ya ajiye wa Kura. Bayan ta dawo sai ya mika mata nama, Kura ta hau ci ba ta san mushe ya dafa mata ba. Ta ci nama, irin cin hadama, amma ta dan rage ta boye a jakarta. Kura ba ta da masaniyar cewa Kurege ya boye nama mai kyau, ya ba ta mushe, Saboda wayo irin na Kurege, sai ya dubi Kura ya ce: "Kura ki rage mini naman mana.
Saboda hadama irin ta Kura ita ma sai ta harari Kurege ta ce: "A'a ba zan ba ka ba tun da kai ne ka dafa, na san sai da ka zabi inda ya fi ko'ina dadi ka ci ka koshi, ba zan kara maka ba." Da rana suka kwanta.
Can cikin dare sai zawayi ya kama Kura. Ta nemi Kurege ya raka taa, sai ya ki, ya ce in zawayin yana damun ta, to ta fita waje. Ya kara da cewa: "Idan ma abin ya dame ki ai sai ki yi shi a kwance ba sai kin tashi ba. Amma idan
na ii ihu to babu lafiya, idan kuma abin ya yi tsanani, idan kuma kin yí shiny to lafiya ke nan.
ta fadi, kuma dare ya yi sai suka sami wata bukkabSai Kura ta fita waje ta yi kwanciyarta. Jim kadan sai kunama ta harbe ta, Kura da raki sai ta kwala kara, haka dai ta kwana tana zawo.
Wayewar gari ke da wuya, sai ta je ta fada wa Kurege cewa jiya da daddare kunama ta harbe ta. Sai Kurege ya ce: “Ai da ma mun yi da ke idan na ji shiru lafiya ta samu, idan kuma na ji ihu to ta yi tsanani sai in fita in taimaka miki."
Bayan Kura ta ji bayanin Kurege, sai ta ce: "To shi ke nan.
Da suka gama maganganunsu, sai Kurege ya rasa yadda zai yi ya daukı naman da ya boye ya kai gida, domin ya sani idan Kura ta gani za ta kwace.
Sai ya yi dabara ya ba Kura shawara ta je ta sha ruwa, ta wanke jikinta kafin su tafi gida. Ba tare da zaton wani abu ba, sai ta kama hanya ta rafi.
Da Kurege ya ga ta tafi rafi, sai ya dauko namansa a inda ya boye, ya saka shi a jakar Kura, shi ma ya shiga cikin jakar. Da ta dawo daga wanka, sai ta dauki jakarta ta rataya. Ba ta san Kurege yana cikin jakar ba, sai ta kama hanya. Dadin waka ya sa ta kama hanyar gida ta fara tafiya, ta manta da Kurege. Tana cikin tafiya sai ta fara yi wa Jakarta waka tana cewa:
Sai ni Kura durungu, Na yi farauta, Na cika jakata da nama, Nama sai mun ture, Ga shi a cikin jakata.
Haka ta rinka yi wa jakar waka. Sai da ta isa gida ta tuna ta bar Kurege a baya, sai ta ga ya kamata ta koma nemansa. Sai t ta ajiye jakarta ta juya ta kama hanyar komawa inda ta fito. Da Kurege ya ga ta tafi, sai ya fia da cikin jakar Kura, rike da namansa ya gudu zuwa gidansa.
Shi ya sa duk wanda ya je daji zai ga Kura tana ta yawon neman Kurege.
Shi kuma da za ku je gidansa, za ku tarar da gidan cike yake da nama mai kyau, wanda yake ci ya more.
Da Kure ya tafi gidansa sai ya kasa barci, ya kagara gari ya waye. Can dai da ya ga kamar gari ya ki wayewa, sai ya hura wuta ta haske ko'ina.
Daga nan ya je ya fada wa Kurege wai gari ya waye, sai Kurege ya ce: "Haba Kure, ka hura wuta a kan dakinka ka ce gari ya waye? Ai gara
koma gida sai gari ya waye.
Bayan ya koma gida ya dan jima gari bai waye ba, sai ya kama zakaran sa aya rinka matsa shi har ya rinka yin cara.
Da Kurege ya fito sai ya ce: Haba Kure yaya kake damun kanka hale ne? Na gaya maka sai gari ya waye.
Haka dai Kure va hakura ala tilas har sai da gari ya waye. Da sassaf.
ya shirya ya nufi kofar gidan Kurege. Suka kama hanyar rafi harnsuka tarar da birrai a bakin rafi. Sai Kure da Kurege suka yanke shawarar sa shiga cikin ruwa su yi wasan kurme.
Da suka shiga tare da birrai sai Kurege ya faki karami daga cikinsu ya danne a ruwa. Shi kuma Kure maimakon ya faki dan karami, sai ya nufi kan babba, ya sa masa igiya ya danne shi. Da ya ji Kure zai halaka shi, sai ya yị Rara, har sauran suka ji, suka watse da gudu.
Kure da Kurege dai kowa ya kaso Biri daya, amma sai Kurege ya ce: Kai kuma Kure da muka yi da kại za ka kama karami don kada su gane, sai ka kama babban cikinsu?"
Sai Kure ya dubi Kurege ya ce masa ai karami ba zai kosar da shi ba, shi ya sa ya kama babba wanda idan ya yi farfesu da shi zai sha ya koshi ya more.
Washe-gari da suka koma tun safe har yamma suna jira a bakin rafinbabu Birin da ya fito bakin rafi. Sai Kurege ya dubi Kure ya ce da shi: "Kai
ka yi mana wannan danyen aiki."
Rannan dai haka suka koma gida, ba su sami nama ba. Sai Kurege ya gaya wa Kure gobe da safe za su je unguwar birrai su gaishe su domin rashin da suka yi na babbansu. Da ma birrai sun aika wa Kurege da Kure za su yi taro domin ba su sani ba cewa ko Kure da abokinsa Kurege ne suka kashe musu 'yan'uwa.
Da gari ya waye suka shirya, sai Kurege ya ce zai hau doki, shi kuma Kure ya hau bera. Sai Kure ya ki, ya ce tun da shi ne babba shi zai hau doki shi kuma Kurege ya hau beran.
Haka aka yi; suka kama hanya, kafin su isa sai Kurege ya ce in sun je chi zai daure abin hawansa a jikin bishiya, sai Kure ya ce shi ne zai daureabiikin bishiya, domin shi ne babba. Sai Kurege ya ce to shi zai daure nasa a
jikin ciyawa.BDa suka isa garin birrai aka yi musu maraba, aka ba su masauki, shl Kure ya daure abin hawansa a gindin bishiya, shi kuma Kurege ya daure nasa abin hawan a jikin ciyawa.
Suna zaune a masauki aka ce za a kawo musu giya don liyafar bafunta. Kafin a kawo sai Kurege ya ce ya kamata su yi waka. Suka fara
waka. Kurege yana rerawa yana cewa: Ni da
Rananan nake wasa,
Da kananan nake abota."
Shi kuma Kure yana waka yana cewa:
Ni da babban nake wasa,
Babba na kama,
A wasan ruwa mai dadi Sai manyan birrai suka ji abin da Kure yake fada, sai suka kawo musu
giva a kwarya. Kure yana ta sha, Kurege kuma ya yi kamar tare suke sha amma in ya zuba a koko sai ya kwara a jikin shinge, shi kuma Kure ya yi ta shan giya har ya yi tilis.
Su kuma manyan birrai suna ta shiri don su rama abin da Kure da Kurege suka yi musu. Nan take birrai suka kwala ihu, suka cea kawo sanduna za đauki fansa. Suka debo sanduna suka nufi kan Kurege da Kure.
Shi kuma Kure ya riga ya yi tilis da giya ta yadda ba ya jin abin da ake fada. Sai ya tambayi Kurege ko me suke cewa a waje?
Sai Kurege ya gaya masa cewa an ce a kawo musu farfesun kashi dabDa Kure ya ji haka sai ya gyara zama, yana dariya da murna wai za a
kawo mnusu nama da kashi.
A daidai lokacin da birrai suka shigo da sanduna za a far ma Kurege da Kure, sai Kurege ya kutsa ta jikin shinge, inda yake kwarar da giya, ya gudu.
Kure kuwa ba zai iva gudu ba. saboda haka suka yi ta jibgar sa.
Bayan Kurege ya fita ta baya, kafin su biyo shi har ya hau kan bera.
Yana taba shi sai ya fara gudu. Shi kuma Kure kafin ya fito ya kwance daga jikin bishiya, ya rigaya ya sha sanduna har ya fadi ya suma.
dokinsa Suka dauke shi, suka đora shi a kan dokinsa, suka kora shi gida. Ya isa gida
a galabaice, ya yi ta jinya da kyar ya warke.
Kurunkus.
Mun dauko wannan labarin daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman