Gwamnatin Zamfara Ta Rufe Wasu Kasuwannin Shanu A Jihar
- Katsina City News
- 03 Sep, 2023
- 1036
Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rufe wasu kasuwannin shanu a kananan hukumomi biyar na jihar nan take.
Kasuwannin shanun da abin ya shafa sun hada da; Danjibga da kunchin kalgo a karamar hukumar Tsafe da kasuwar shanu ta Bagega da Wuya a karamar hukumar Anka da Dangulbi da Dansadau a karamar hukumar Maru da Dauran a karamar hukumar Zurmi da kuma Nasarawar Burkullu a karamar hukumar Bukkuyim.
Rufe kasuwannin na kunshe cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Manir Haidara, ya fitar, kan daukar matakin rufe kasuwannin shanu na wani dan lokaci biyo bayan taron majalisar tsaron jihar.
A cewar sanarwar, “rufe kasuwar shanun ya samo asali ne sakamakon munanan ayyukan ta’adda na sayarwa da lodin satar shanu da wadanda ake zargin ‘yan fashin daji ne ke yi.”
Majalisar tsaron ta yi kira ga hukumomin tsaro da hukumar kula da lafiyar dabbobi da kiwo da su tabbatar da bin doka da oda.
Majalisar ta bukaci jama’ar gari da masu ruwa da tsaki da su jajirce wajen sa ido da don inganta zaman lafiya a kasuwanni shanu da ke Jihar.