Tatsuniya (9); Labarin Budurwa Mai Neman Ganyen Miya
- Katsina City News
- 17 Apr, 2024
- 786
Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wata budurwa mai suna Yakadi a wani dan kauye da ke nan kusa da bakin rafi. Wata rana sai mahaifanta suka aike ta lambu ta samo ganyen miya. Ta shirya ta kama hanya tare da kannenta, suka je, suka samo ganyen
miya.
A kan hanyarsu ta dawowa gida sai suka hadu da wata tsohuwa ta ce da su: "Sannunku 'yan mata, don girman Allah ku taimake ni da ganyen dan kadan mana.
Sai ita Yakadi ta ce: "Ba za a bayar ba."
Suka ci gaba da tafiya, da suka kai kusa da wani dutse sai suka ce za su huta. Bayan sun zauna sun huta, sai kannenta suka tashi tsaye za a fara tafiya. amma ita Yakadi sai ta kasa tashi domin duwawunanta sun manne a jikin dutse. Suka yi kokarin banbare ta domin su tayar da ita amma suka kasa.
Da suka gaji, sai suka bar ta a can, suka nufi gida da gudu don su sanar da iyayensu abin da ya faru. Da iyayen suka ji haka, sai suka kama hanya har inda 'yarsu ta makale. Suna isa, suka yi ta kokarin ciro ta, amma abu ya gagara. Sai suka yanke shawarar gina daki a kanta, haka kuwa aka yi.
Tana can, kullum suna kai mata abinci.
Duk sanda mahaifiyarta ta je wurinta a dakinta, sai ta yi wata waka, in ta ji muryar mahaifiyarta ne sai ta bude mata kofar daki ta shiga, in kuma ta Ji wata murya ce daban, sai ta ki budewa.
Haka ta ci gaba da rayuwa har zuwa wani lokaci da Kura garin yawo ta tarar da dakin da Yakadi ke ciki, ta yi kokarin shiga, amma ta kasa. Dayan 'yan matan kauyen suka fita kamun kifi wannan budurwa da takan ba tsohuwa kifi.
Yadda aka yi ta samo kifin nan kuwa shi ne, da ta kama hanyar rafi sai ta hadu da wannan tsohuwar. Sai tsohuwa ta ce mata kada ta je babban rafi tsohuwa ta ce ta yashe ruwan.
Da budurwa marainiya ta fara yashewa sai ta
ta nuna mata wata hanya da za ta kai ta har bakin wani karamin gulbi. Sai fara ganin manyan kifaye, ta yi ta diba har kwaryarta ta cika, ta koma gida. A duk fadin garin budurwar nan kadai ce ta kamo kifi a wannan rana. Bayan ta dafa kifi ta sa a cikin akushi ta kai fada, mutanen gari da Sarki suka yi kifi, amma ba wadda ta samo Sai mamaki. Nan take Sarki ya amince zai aure ta.
Bayan ta koma gida sai aka gaya mata ta sanar Za a yi bikinta da Sarki. To da yake iyayenta duk duk sun rasu marainiya ce, ba ta da kowa, da ta koma gida dare ya yi ta kwanta, sai ta tashi tsakar dare tana luke domin tana tunanin ba wanda zai yi mata kayan gara. Tana cikin wannan hali na damuwa, sai ta ga kwatsam tsohuwar nan ta bullo mata a tsakiyar daki, kuma ta tambaye ta ko mene ne yake damun ta. Sai marainiya ta yi mata bayanin dukkan abin da yake damun ta, har ya zamanto ba ta iya yín barci. Da yar tsohuwa ta lallashe ta sai kuma ta gaya mata za ta kawo mata dukkan abin da take bukata. Yarinya ta yi ajiyar zuciya cikin murna, ta yi wa tsohuwa godiya. Tun kafin gari ya waye, sai ta ga dakinta cike da kayan
gara fiye da yadda take zato za ta samu, ta yi ta murna. Ta gode wa Allah. Ana nan, ana nan, ranar bikinta da Sarki ta zo, aka daura musu aure, aka yi gagarumin biki, aka kai amarya gidan Sarki da gararta. Bayan biki ya kare sai tsohuwa ta sake bullo mata a dakinta, ta kuma kawo mata kayan alatu da na marmari. Ta ce mata kullum za ta rinka kawo mata kayan dadi
ta rinka ba Sarki, amma kada ta gaya wa kowa. Yarinya ta ce ba za ta gaya wa kowa ba.
Suka yi sallama tsohuwa ta tafi. Bayan 'yan kwanaki sai matan Sati suka fara tsegumi cewa amarya ba ta da kowa, amma kullum Sarkı yana kara son ta fiye da sauran matansa, kuma kayan alatu da take ba Sarki wa hakura, suka bar ta. da iyayenta, yake ba ta? Suka yi ta bincike, amma ba su gano bakin zaren ba, sai suka To shi Sarkin bai taba haihuwa ba, duk sanda matansa suka dauki cikl, sai ya zube. Rannan bayan 'yan shekaru da auren marainiya da Sarki, sai ya tara matansa, bayan ya tabbatar kowacce tana da ciki. Ya ce d da su kowacce ta tafi gidan iyayenta, kuma kada ta dawo sai ta haihu. tana cewa: Bayan kowacce ta kama hanyar gidansu, sai ita kuma amaryar Sarki marainiya ta tafi gindin wata tsamiya ta zauna, ta kamna kuka, tana waka
Wa zai ba ni yaro a yau?
Wa zai amshi haihuwa a yau?
Ni ba ni da uwa, ni ba ni da uba?
Tana cikin wannan hali sai tsohuwa ta zo ta sake tambayar ta abin da yake damun ta. Sai ta kwashe labarin yadda suka yi da Sarki ta gaya mata. Sai tsohuwa ta dauke ta, ta kai ta gidanta, ta ci gaba da kula da ita, tana yi
mata albishirin cewa in Allah ya yarda, za ta haihu, cikin ba zai zube ba. nan tare da tsohuwa har ranar haihuwa ta zo, ta haifi danta
Lafiyayye. kowa ya gan shi ya ga ubansa.
Amma sauran matan Sarki kuwa
ba su sami haihuwa ba, sai daya daga cikin kishiyoyínta ta sami labarin haihuwar amaryar Sarki marainiya, Sai ta fara bin ta a sace, har ranar da aka sa za su koma gidan Sarki.
Dannan sai amaryar SarkI ta tafi bakin rafi don ta yi wanka tare da đanta Da ta je bakin rafin sai ta ajıye jaririn, ta shiga wanka. Sai kishiyar nan tata ta zo ta sace yaron, ta gudu da shi.
Da suka koma fada sai amaryar Sarki marainiya ta je ta gaya wa Sarki cewa ta haihu, amma an sace abin da ta haifa. Sai aka k i yarda da wannan
magana. Da kishiyarta wadda ta sace yaron ta zo, sai suka ce ita ce ta haifi yaron. Ita kuwa matar Sarki marainiya sai aka sa fadawa da yaran Sarki suka kafa mata daki irin na dawaki, aka ajiye ta a can, bisa cewa ta yi wa Sarki
karya. Da kishiyarta ta ba yaron nono sai ya ki kamawa. Aka yi juyin duniyar nan, jaririn nan ya ki shan nono, sai aka rinka ba shi madarar shanu. Ana nan, ana nan, wata rana sai dan duba watau Sarkin bokayen Sarki, ya gaya wa Sarki cewa wannan da nasa matar da ta rene shi ba ita ce uwarsa ba. Mamaki ya kama Sarki, sai ya nemi Sarkin bokaye da ya gaya masa
ta yadda zai gane uwar yaron. Sai mai duba ya ce ya tara matansa ranar kasuwar garin, kuma a tara mutane a fada, sannan duk matansa su yi abinci, su kawo shí bainar jama'a, kuma su jeru a fada. Idan an yì haka, sai a ce da yaron ya zabi abincin da matan Sarki suka kai wurin, to duk abincin da yaron ya zo ya ci, tabbas mai wannan abinci ita ce uwarsa. Ba tare da nuna wata shakka ba, Sarki ya ce a yi haka din. Sarki ya umarci matansa a kan abin da ake so kowacce ta yi. Duk matan suka yi dare-dafen kayan dadi. Ranar kasuwa ta zo, mutane suka taru, fada ta cika ta batse. Amma ita amaryar Sarki marainiya, kuma uwar yaron ta gaskiya,
ba ta da abin da za ta dafa. Hasali ma tun ranar da aka kai ta dakin dawaki ba ta cin komai sai in an zuba wa doki dusa ta diba, ta dama ta sha, ko ta 3 tuwo da ita, Da aka ce har ita ma sai ta yi abinci, sai ta debi dusar da aka
Adakawa dawaki kamar yadda ta saba. ta kama gafiya ta yanka, ta gyara ta da kyau, ta dauka ta kai fada. Da la isa fada sai ta tarar duk sauran matan Sarki sun jeru, suka shiga nata kallon reni da nuna mata kyama. Can da dan Sarki ya zo a kan doki har ya girma.
Aka ce ya zabi abincin wadda zai ci daga cikin matan Sarki, sai kawai yo karya linzami ya doshi inda mahaifiyarsa marainiya take. Da zuwa sai ya kama cin abincin dusar nan da ke gabanta.
Da mutanen da suka yi cincirindo a fada suka ga haka, sai mamakin yadda al'amarin ya kasance ya kama su. Da Sarki ya ga alama lallai gaskiya ce ta yi halinta, sai ya sa aka kama matar da ta yi satar yaron ta ce nata ne, aka fille mata kai. Ita kuwa mahaifiyar yaron ta gaskiya sai Sarki ya ba ta hakuri, ya nemi ta gafarta masa ya Ba dade da yin wannan abu ba, Sarki ya kamu da rashin lafiya, wadda
ta zama ta ajalinsa. Bayan an gama zaman makokin rasuwar Sarki, sai aka nada shi dan marainiya a matsayin sabon Sarki. A cikin ikon Allah yaronya hau karagar mulki. Ya ci gaba da tafiyar da harkar mulki kuma 'yar tsohuwar nan da uwarsa zumuncin da yake tsakaninsu ya kara karfi.
Kurunkus.
Mun dauko wannan labarin daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman