GWAMNAN ZAMFARA YAYI HAWAN DABA A KAURAN NAMODA.
- Katsina City News
- 15 Apr, 2024
- 555
@ KATSINA TIMES
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya halarci bikin hawan Durbar a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda a ranar Lahadin nan.
Masarautar Ƙauran Namoda na gudanar da wani gagarumin biki na musamman bayan Sallar Idi, wanda aka fi sani da Hawan Durbar duk shekara.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa, bikin hawan Durbar na haɗa jama’a domin murnar zagayowar ranar sallah da kaɗe-kaɗe, raye-raye, da sauran al’adun gargajiya.
Sanarwar ta ce, a yayin bikin hawan Durbar mai ban sha'awa, an naɗa Gwamna Lawal sarautar 'Wakilin Kaura', wanda ke nufin wakilin wanda ya kafa masarautar.
“Gwamna Dauda Lawal ya halarci bikin hawan Durbar na Masarautar Ƙauran Namoda a yau.
“Hawan Durbar wani biki ne mai ban-sha’awa wanda ke nuna al’adun gargajiyar masarautar Ƙauran Namoda. Hawan Durbar da ke Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda tana bai wa jama'a damar haɗuwa waje guda, tare da taya murna zagayowar sallar wannan shekara.
“Bikin Durbar na bana ya zama mai matuƙar muhimmanci ga masarautar, domin wannan ne karon farko da wani gwamna mai ci a jihar ya halarci taron.
“Gwamna Lawal, sanye da kayan gargajiya, ya shiga hawan Durbar a lokacin da yake kan dokin da aka ƙawata da kayan ado.
“A lokacin da ake gudanar da bikin, Sarkin Ƙauran Namoda, wanda aka fi sani da Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda, Dokta Sanusi Muhammad Ahmad Asha ya bai wa Gwamna Dauda Lawal sarautar gargajiya ta Wakilin Ƙaura, wato wakilin wanda ya kafa masarautar. Wannan karimcin ya nuna godiya ga halartar gwamnan a wajen bikin.”
Sannan Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da ƙofar birnin Modomawa, tsohuwar ƙofar Kauran Namoda tun daga 1807-1810.
Ya kuma duba cibiyar kula da gidan talabijin ta Nijeriya NTA a Ƙaramar Hukumar, inda ya yi alƙawarin bayar da duk wani tallafin da ya dace don farfaɗo da tashar.