TATSUNIYA (8) Labarin Budurwa mai neman ganyen miya
- Katsina City News
- 14 Apr, 2024
- 404
Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wata budurwa mai suna Yakadi a wani dan kauye da ke nan kusa da bakin rafi. Wata rana sai mahaifanta suka aike ta lambu ta samo ganyen miya. Ta shirya ta kama hanya tare da kannenta, suka je, suka samo ganyen
miya. A kan hanyarsu ta dawowa gida sai suka hadu da wata tsohuwa ta ce da su: Sannunku 'yan mata, don girman Allah ku taimake ni da ganyen dan kadan mana.
Sai ita Yakadi ta ce: “Ba za a bayar ba."
Suka ci gaba da tafiya, da suka kai kusa da wani dutse sai suka ce za su huta. Bayan sun zauna sun huta, sai kannenta suka tashi tsaye za a fara tafiya. amma ita Yakadi sai ta kasa tashi domin duwawunanta sun manne a jikin dutse. Suka yi kokarin ban6are ta domin su tayar da ita amma suka kasa.
Da suka gaji, sai suka bar ta a can, suka nufi gida da gudu don su sanar da iyayensu abin da ya faru. Da iyayen suka ji haka, sai suka kama hanya har inda 'yarsu ta makale. Suna isa, suka yi ta kokarin ciro ta, amma abu ya gagara. Sai suka yanke shawarar gina daki a kanta, haka kuwa aka yi. Tana can, kullum suna kai mata abinci.
Duk sanda mahaifiyarta ta je wurinta a dakinta, sai ta yi wata waka, in ta ji muryar mahaifiyarta ne sai ta bude mata kofar daki ta shiga, in kuma ta Ji wata murya ce daban, sai ta ki budewa.
Haka ta ci gaba da rayuwa har zuwa wani lokaci da Kura garin yawo ta tarar da dakin da Yakadi ke ciki. ta yi kokarin shiga, amma ta kasa. Ana nan, wata rana Kura ta buya, ta ji irin yadda uwar yarinya take yin waka a bude. ta shiga. Bayan uwar yarinyar ta tafi, sai Kura ta je ta yi wakar, to amma da yake muryar ba irin ta uwar yarinyar ba ce, sai ta ki budewa.
Da Kura ta ga haka, sai ta tafi inda ake gyaran murya, aka gyara mata. A kan hanyar zuwa inda Yakadi take, sai yunwa ta kama Kura. Da ta ga Ruda, sai ta kama shi ta hadiye.
Da Kura ta isa kofar dakin, ta fara waka sai muryarta ta shake, ta koma kamar ba a gyara ba. Yarinya kuwa ta ki bude kofa, Kura kuwa ta sake komawa wajen gyaran murya, mai gyara ya ce mata in ta kama hanya kada ta ci komai, sai ta yi wakar ta gama. Sai Kura ta yarda, ta kama hanya.
Kura tana cikin tafiya, sai yunwa ta sake kama ta. Da ta ga sauro, sai ta kama shi, ta hadiye. A nan ma muryar Kura ta sake 6aci, ta koma wajen masu gyara a karo na uku, masu gyara suka sake gyara mata murya, suka hada ta da mai kula da ita har sai sun je bakin dakin da yarinya take.
Da yake Kura ba ta ci komai a hanya ba da ta yi waka a kofar dakin Yakadi, sai ta ji murya kamar ta mahaifiyarta, ta ja kofa ta bude. Kura ta shiga ta cinye ta, amma ta bar kai da kafafu.
Bayan Kura ta tafi, sai uwar yarinya ta je, ta tarar an cinye yarta, in ban da kai da kafafu. Sai ta fara kukan bakin ciki. Tana cikin kuka sai
tsohuwar nan ta zo ta rarrashe ta, kuma ta gaya mata idan ta je gida ta kona kai da kafafun Yakadi ta zuba tokar a kwarya mai yoyo, idan tokar ta fara zuba saí ta rinka kiran sunayen gangar jikin Yakadi daya bayan daya, harbsai yarta ta hadu, Sai ta yi wa tsohuwa godiya, ta tattara kai da kafafun "yarta, ta koma gida.
Da ta koma gida sai ta yi yadda tsohuwa ta umarci ta yi. Da ta fara kiran Sunaye bangarorin jikin 'yarta, sai duk bangaren da ta ambata ya fado, nar dai ta gama kiran dukkan sauran sassan jikin yarinya, sai ta ga 'yarta ta dawo da rai kuma kyakkyawa kamar yadda take a da, ta ci gaba da rayuwa har lokacin da aka yi mata aure.
Kurunkus.
Mun dauko wannan labarin daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman