TATSUNIYA (7): Labarin Dagaci da Malaminsa
- Katsina City News
- 12 Apr, 2024
- 484
Ga ta nan, ga ta nanku.
An yi wani Dagaci a wani gari yana da matarsa, to amma matar ba ta taba haihuwa ba. Ba tare da saninsa ba, wata rana matar wani babban
malami ta je wurin matar Dagaci hira a gidansa.
Suna cikin hira sai matar dagacin ta fara ba matar malamin labarin tashin hankalin da take ciki na rashin haihuwa. Kuma ga shi mai gidanta, watau Dagacin, ya ce yana son ya sami 'ya' yan da za su zo su gaje shi. Kuma ya ba matar tasa wasu 'yan watanni, idan ba ta sami ciki ba zai kore ta, ya auro wata matar. Wannan barazana ce fa ta sa matar Dagaci ta fara kuka da bakin ciki.
Da matar malami ta ji yadda labarin yake, sai ta tausaya wa matar Dagaci. Shi ke nan, sai matar malamin ta ce mata: Kin ga ni yanzu ina da
ciki wata biyu, sai ki fara dunkula tsumma ki daura a cikinki ki gaya wa mijinki cewa Allah ya ba ki juna biyu."
Abin da matar malami take son yi shi ne idan Allah ya sauke ta lafiya, za ta kawo wa matar Dagaci abin da ta haifa, domin ta nuna wa mai gidanta cewa ta haihu.
Wannan hikima ta faranta wa matar Dagaci rai, kuma ta yarda aka yi alkawari da matar malami, har matar Dagaci ta durkusa tana yi mata godiya. Bayan 'yan kwanaki sai ta gaya wa Dagaci cewa ta yi batan wata, kuma tana tsammani tana da ciki wata biyu. Da Dagaci ya ji wannan labari sai ya shiga murna, Ya fara fada wa fadawansa da mutanen gari cewa yanzu kam matarsa tana da juna biyu, kuma in Allah ya yarda ba da dadewa ba za ta haifa masa dan da zai gaje shi.
Saboda farin cikin da Dagaci yake yi, sai ya ba da umarni a kai matarsa wani gyararren gida. Ya sa a rika yi mata duk abin da take so. Kuma ya ce kada ta taka ko kofar daki don kada ta wahala a lokacin da take renon cikin har ranar haihuwarta. Ana nan sai mutane suka fara tsegumi a kan ai da ma matar Dagaci ba ta haihuwa, yaya kuma yanzu za a ce tana da ciki? Surutai suka yi yawa a gari, har wasu suka bugi kirji, suka sami Dagaci suka fara yi masa irin wannan magana. Wani daga cikinsu ya ce, idan matar Dagacin nan ta haihu, to a dauki rumbın zuba amfanin gonar gidan Dagaci a dora masa a kansa. Wani kuma ya ce, in ta haihu a daura masa igiya a kwankwaso a zagaya gari da shi har ya mutu. Can na ukunsu ya ce, in har ta haihu, to zai cinye buhun barkono goma shi kadai.
Wani kuma ya ce, shi idan ta haihu to zai cinye dutsen da yake bayan gari. Haka dai suka ci gaba da maganganu, shi kuwa Dagaci bai ce komai ba, aka ci gaba da renon ciki har ya kai lokacin haihuwa.
A ranar da matar malami ta haihu sai aka ce ai matar Dagaci ta haihu. Kamar yadda aka yi alkawari, sai matar malami ta dauki jaririnta ta kai wa matar Dagaci ba tare da wani ya san an yi haka ba. Bayan labari ya bazu a gari sai masu rantsuwa suka dawo gaban Dagaci suka ce har idan an fito da yaro aka yi masa aski ranar suna, to za su cika alkawarin da suka dauka, amma idan kuma zancen karya ne, to za a kashe matar Dagaci. Dagaci ya yarda da haka.
Matar Dagaci ta ci gaba da renon jaririn matar malami har ranar suna ta zo. Ana gobe suna sai matar malami ta dawo ta ce mijinta ya ce shi ba zai babda đansa ba, saboda haka a dawo masa da dansa. Matar Dagaci na jin haka, sai ta ce: "Haba matar malam, bayan mun gama magana da ke kuma kin dauki alkawari yanzu ki dawo ki ce ba zai yiwu ba, ai wannan cin amanabane. Idan Dagaci ya ce ina jariri bayan kowa ya ji na haihu, to me zan gaya wa Sarki? Kuma an ce idan ba a fita da yaro ba gobe ranar suna, za a kashe ni. Ki yi min rai mana!" Haka dai ta yi, ta yi, amma matar malami ta ki yarda, daga karshe ta karbi danta ta tafi gida, matar Dagaci ta rasa yadda za ta yi. Da ta ga ba mafita sai ita da kanwarta suka shirya za su gudu cikin dare. Da dare ya yi suka kama hanyar daji suna cikin tafiya, sai suka ji wata tsawa a gabansu sai suka ga kasa ta tsage, sai ga wani jariri a cikin tsumma yana kuka. Sai matar Dagaci ta yi godiya ga Allah, ta dauki yaro suka kama hanyar gida.
Ba jima da komawa gida ba gari ya waye.
Fada kuwa ta cika fal da mutanen gari da makada da mawaka da wanzamai za a yi wa dan Dagaci aski, kuma a rada suna. Su kuma masu alkawari suna gefe suna jiran burinsu ya cika a ce babu yaro. Sai Dagaci ya tura a kawo jariri. Aka shiga cikin gida aka fito da yaro kyakkyawa mai kama da Dagaci. Nan take wadanda suka dauki alkawari idanu suka raina fata.
Shi kuma malami mamaki ya kama shi, aka dai yi wa yaro aski, aka rada masa suna. Sarki ya sa aka kamo wadanda suka dauki alkawari aka fara hukunta su, dai-dai da dai-dai, har suka mutu. Shi kuma malami ya kama hanyar gida ya kwashe labari ya gaya wa matarsa yadda aka yi. Sai malami ya ce da matarsa ta dauko yaron su ma su rada masa suna. Da ta je ta dauko yaro, sai ta tarar ya mutu.
Matar malami kuma bakin ciki ya kama ta, ta kama hanyar gidan Dagaci. Da ta shiga ta sami matarsa sai ta yi ta ba ta hakuri game da laifin da ta yi mata. Ita ko matar Dagaci ta ce ba
komai, zance ya wuce, ta ci gaba da zaman dadi da mijinta har lokacin da mai rabawa ta raba.
Kurungus
Ga bera nan, ga 6era nan, duk wanda ya ji tsoro alhaki a kansa.
Munciro wannan labarin a cikin littafi Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman.