TATSUNIYA (7): LABARIN MACE MAI CIKI
- Katsina City News
- 11 Apr, 2024
- 666
Ga ta nan, ga tananku.
Wata rana wata mata mai juna biyu ta je dibar ruwa a bakin rafi. Bayan ta cika tulunta da ruwa, sai ta kasa dauka saboda cikinta ya girma sai nishi take yi, abin tausayi. Kuma ga shi ita kadai ce kwal a wurin.
Haka ta hakura ta zauna. Can sai ga wani mutum ya taho, sai ta dube shi ta ce: Malam don girman Allah ka dora ni mana.
Sai ya ce shi ba zai dora ta ba sai dai idan za ta yi masa wani alkawari. Mai ciki ta dube shi ta ce: Na mene ne?
Shi ko ya ka da baki ya ce: Idan kin haihu, in namiji ne to abokina ne, idan kuma mace ce, to matar dana ce." Da jin wannan sharadi sai ta yarda. Ya dauki tulu ya dora mata ta kama hanya ta tafi gida. Da ta je gida sai ta yi
wa mijinta bayanin yadda suka yi da mutumin.
Da yake mijinta mai saukin kai ne, bayan 'yan kwanaki sai mutumin ya zagayo gidan matar, suka gaisa. Ya nuna mata dansa suka yi sallama ya koma gida, Bayan wata daya sai
matar ta haifi 'ya mace, amma jikinta na jaki ne.
Duk da haka sai ya yi halin dattaku ya ce: To shi ke nan tun da mutumin ya ga haka yi alkawarı ai sai ya sauke. Sai ya kira dansa aka daura musu aure da yarinyar ya kai ta gidansu.
Yaro ya zauna da mace mai jikin jaki. Ya daure ta a gida. Amma duk sanda ya tafi gona idan ya dawo gida sai ya tarar an yi masa shara, an dafa masa abinci da kuma kai masa ruwan wanka bayan daki.
Kullum haka, sai abin ya fara ba shí tsoro tun da ba kowa a gidan.
Rannan sai ya je ya sami babansa ya gaya masa, amma sai baban ya ki kula shi sai ya kore shi.
To da ma yaron yana mutunci da wata tsohuwa makwabciyarsa dangarsu daya. Sai wata rana ya zauna a gindin bishiya, yana tunanin abin
mamakin da ke samunsa.
Da tsohuwar ta gan shi a zaune haka, sai ta kira shi ta ce: Dan yaro
me ke damunka ne?" Shi ko sai ya kwashe labari ya bai wa wannan tsohuwa.
To da ma ashe tsohuwa tana ganin duk abin da yarinya take yi idan ya tafi gona. Watau rikida take yi ta koma kyakkyawar budurwa, ta shiga yi masa waka, ta yi shara, ta yi wanke-wanke, ta dafa abinci, ta debo ruwa a rijiya ta kai masa ban daki. Duk bayan ta gama kafin ya dawo sai ta mayar da jikinta na jaka, ta daure kanta a turke. Da tsohuwa ta gama bai wa yaron labarin abin da take gani sai ta shawarce shi da cewa gobe ya kwashi kayan aiki kamar zai tafi gona, idan ya kama hanya sai ya ratse a hanya, ya zagayo gidanta. Bayan sun gama shirya zancensu, sai ya koma gida yana mamaki, ya shiga daki ya kwanta.
Da gari ya waye sai ya saka kayan aiki ya dauki fartanyarsa ya kama hanyar gona. Bayan ya tafi ya yi nisa sai ya ratse cikin ciyawa, ya zagayo ta gidan tsohuwa, ya same ta a daki.
Daga nan sai suka 6uya suka shiga leken yarinyar. Jim kadan sai suka ga ta rikida ta koma kyakkawar mace, ta fara waka ta kama shara da sauran ayyukan gida, ta shirya miya, ta dafa abinci, ta zuba nasa, ta kai masa ruwan
wanka ban daki. A daidai lokacin da ta fito daga bayan gida sai mijinta ya tsallaka danga
ya dira a gabanta, Sai kawai ta razana za ta rikida sai ya kama hannunta ya fara yi mata waka yana rokon ta.
Da ta ji wakarsa sai ta fara kuka tana rokon ya yafe mata, Shi ke nan suka yi zamansu cikin dadi suka ci gaba da more rayuwarsu cikin Kauna da farin ciki.
Kungurus
Daga littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman