Gwajo-gwajo ya yabawa gwamnatin jihar Katsina bisa rabon tallafin watan Ramadan
- Katsina City News
- 09 Apr, 2024
- 422
Mai bawa Gwamna Dikko Umar Radda shawara na musamman kan harkokin siyasa Rt. Hon. Ya’u Umar Gwajo-Gwajo, ya yabawa gwamnatin jiha karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda kan rabon tallafin abinci ga al’ummar jihar a cikin wannan wata na Ramadan.
Ya bayyana tallafin a matsayin wanda ya dace, duba da irin wahalhalun da ake fuskanta sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da tsadar kayan abinci a kasar.
Gwajo-gwajo ya bayyana cewa tallafin abinci ya taimaka wajen rage farashin kayan abinci a jihar tare da samar da abinci ga marasa galihu.
Ya ce matakin ya nuna irin tausayin da Gwamna Dikko Radda yake da shi ga al’ummar jihar wanda ya yi daidai da alkawarin da ya yi a yakin neman zabe na samar da jin dadin jama’ar sa.
Mai ba da shawara kan harkokin siyasa ya bukaci al’ummar Jihar Katsina da su yi amfani da lokacin Sallah wajen yi wa Gwamna Dikko Radda da Shugaba Bola Ahamed Tunubu addu’a domin samun nasarar cika alkawuran da suka dauka a lokacin yakin neman zabe.
Ya kuma bukace su da su yi addu’ar samun zaman lafiya da tsaro a sassan jihar da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.