Watan Ramadan: Gwamnan Jihar Katsina ya fitar da Bursunoni 222 daga gidan Kaso
- Katsina City News
- 08 Apr, 2024
- 563
A ranar Litinin 8 ga Afrilu, 2024 a cikin shirinsa na azumin Ramadan da goron-Sallah, Gwamna ya biya tarar fursunoni 222 da ke gidajen gyaran hali daban-daban a fadin jihar Katsina, wadanda ake tsare da su saboda kasa biyan kudin tarar da kotuna daban-daban su ka sanya musu.
Fursunonin da aka ɗauka waɗanda ke da ƙananan laifukan da suka danganci kasuwanci ne da sauran kananan laifuka. An tantance fursunonin da suka samu wannan damar, kuma an ba da shawara ga gwamnatin jihar domin ta shiga tsakani don biyan kudaden da su ka yi sanadiyar rike su a gidajen gyaran hali.
Matakin da gwamnatin jihar ta dauka zai rage cunkoso a gidajen gyaran hali sannan kuma zai baiwa fursunonin da aka sako damar yin bukukuwan Sallah tare da ‘yan uwansu.