Yadda Sabbin Gwamnoni 13 Suka Lafto Wa Jihohinsu Bashin Biliyan 226 Cikin Wata 6
- Katsina City News
- 07 Apr, 2024
- 406
Khalid Idris Doya
Akalla sabbin gwamnonin jihohin Nijeriya 13 ne suka karbi bashi biliyan 226.8 a cikin gida da waje cikin watanni shida kacal bayan sun hau karagar mulkin jihohinsu daban-daban, kamar yadda rahoton hukumar kula da basuka (DM0) ta fitar.
Rahoton hukumar DMO ya yi amfani da kididdigar basukan waje bisa la’akari da canjin dala kai naira 889.
Basukan wadanda suka hada da rancen cikin gida da masu ba da lamuni na kasa da kasa irinsu babban bankin duniya da kuma asusun bayar da lamuni ta duniya (IMF).
Rahoton hukumar DMO ta wallafa a shafinta zuwa ranar 20 ga watan Disamba 20 da 30 June 2023 ne aka kiyasce wannan adadin basukan.
Jerin jihohin da suka lafto wannan makudan kudaden a matsayin rance su ne, Jihar Benuwai, Kurus Ribas, Katsina, Neja, Filato, Ribas, Zamfara da kuma babban birnin tarayya wadanda suka samu biliyan 115.57 daga hannun masu ba da lamunin na cikin gida, yayin da gwamnonin Ebonyi, Kaduna, Kano, Neja, Filato, Sakwato, Taraba da Zamfara suka ciwo basukan dala miliyan 125.1, kimanin naira biliyan 111.24 daga masu ba da rance na waje.
Rahoton ya ci gaba da ba da bayani da cewa gwamnan Kurus Ribas, Bassey Out shi ne ya ciwo bashi mafi yawa a tsakanin wannan lokacin da ya kai naira biliyan 16.2, na bashin cikin gida da kuma dala miliyan 57.95 daga masu ba da lamuni na waje a tsakanin watan June zuwa Disamban 2023. Gwamnan Jihar Katsina ne ya biyo bayansa da ciwo bashin naira biliyan 36.93 da ya karu daga biliyan 62.37 zuwa biliyan 99.2 a watan Disamban 2023.
Jiha ta uku kuwa ita ce Jihar Neja da ta ciwo bashin cikin gida na naira biliyan 17.85 da ya karu daga biliyan 121.95 a June na 2023 zuwa biliyan 139.8 a watan Disamba.
Jihar Filato kuwa, bashin naira biliyan 16.32 ta ciwo, Ribas ta lafto wa kanta rancen naira biliyan 7.07, Zamfara kuwa naira biliyan 14.26 ta ciyo, yayin da birnin tarayya a karkashin jagorancin Nyesom Wike ta ciwo bashin naira biliyan 6.75 daga masu ba da lamuni na cikin gida.
A basukan waje kuwa, gwamna Jihar Ebnonyi, Francis Nwifuru ya amshi bashin dala miliyan 37.54, yayin da gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya karbi dala miliyan 17.69 daga masu ba da lamuni na waje.
Bugu da kari, gwamnonin Kano ya ci bashin dala miliyan 6.6, Neja dala miliyan 1.27, Filato dala 831,008, Sakkwato dala 499,472, Taraba dala miliyan 1.51, da kuma Zamfara mai bashin dala 655,563 daga masu ba da rance na waje.
Daga shafin Leadership Hausa na yanar gizo