Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta Hana Ayyukan Ɓadala tare da sa Ido ga masu Aikatawa
- Katsina City News
- 07 Apr, 2024
- 651
Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, karkashin Jagorancin babban kwamanda na jihar Katsina Dakta Aminu Usman (Abu Ammar), ta Ayyana wasu ayyukan baɗala 4 a matsayin haramun tare da daukar matakai akan masu yi.
Ayyukan Baɗalar da suke kara ruruwa kamar wutar daji a jihar Katsina ga matasa wanda Hukumar ta Hana sun hada da.
1. Ayyukan Kide-kide na DJ
2. Sara Suka (Ƙauraye)
3. Wasan Galla
4. Gudanar da bukukuwan Aure da suka sabawa shari'a
A yunkurin da hukumar Hisbah ta ke na tabbatar da tsaftar Al'umma, ta sake jaddada aniyar ta na sa ido da kuma tabbatar da bin doka a fadin jihar.
Hukumar Hisbah ta hada kai da jami’an tsaro na jihar Katsina, ta yi alkawarin daukar kwararan matakai na kawar da duk wata barna da rashin da’a a jihar Katsina. Hukumar ta bukaci iyaye, malaman addinin Islama, da shugabannin al'umma da su kasance a faɗake tare da ba da goyon baya ga kokarin jagoranci da kula da matasa.
Sa hannu:
Mallam Nafi'u M. Aƙilu
Jami'in Hulda da Jama'a
Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina
- Afrilu 7, 2024 -