Tatsuniya: Labarin Wani Sarki Da Matansa
- Katsina City News
- 05 Apr, 2024
- 434
Ga ta nan, ga ta nanku.
Wani Sarki ne mai mata uku, amma Allah bai taba ba shi haihuwa ba. Ana nan, ana nan wata rana sai ya nemi shawarar fadawansa a kan abin da ya kamata ya yi saboda wannan rashin haihuwa. Sai suka ce ya kamata ya kara aure. Shi ko ya dauki shawararsu, ya sa aka nema masa budurwa kyakkyawa ya aure ta.
Bayan wasu 'yan watanni sai Allah ya ba ta ciki, labari kuma ya gama ko'ina, matar Sarki tana da ciki. Su kuwa kishiyoyinta sai suka shiga bakin ciki, don sun dade a gidan Sarki ba tare da ko daya daga cikinsu ta sami ko da batan wata ba.
Daga nan sai suka shiga neman hanyar da za su bi su zubar da cikin, amma abu ya gagara, har lokacin haihuwa ya zo. Lokacin da suka tabbatar ta kusa haihuwa, sai suka je wurin Sarki suka nemi izini su je shan iska da saran itace a jeji tare da bayinsu. Ba tare da wani mugun zato ba, sai Sarki ya ba su izini, amma da sharadi, ba za su je da amaryarsa mai juna biyu ba. Sai suka ce ai za su kula da ita, kuma babu abin da zai same ta.
Da suka nace, sai Sarki ya bar su suka tafi jeji da ita. A dajin nan nakuda ta kama ta, suka kai ta gindin bishiya, suka kwantar da ita, ta haihu. Da suka ga ta haifi 'ya kyakkyawa, kuma ba ta cikin hayyacinta, sai suka dauki jaririyar suka jefa a kan bishiya. Can da rana ta yi sanyi, sai su da bayinsu suka kama hanyar gida, tare da mai jego.
Lokacin da suka isa gida, sai matan Sarki suka je turakarsa, suka gaya masa wai matarsa ta haifi wani dan itace ne, ba mutum ta haifa ba. Da jin wannan bayani sai ya fusata, domin ya dauka gaskiya suka gaya masa, ya sa aka kai amaryarsa wani gida ita kadai inda ba kowa, sai abin tsoratarwa, aka bar ta a can. Bayan wasu 'yan watanni sai bayin Sarki suka je daji yanko wa dawakin Sarki ciyawa. Suna cikin yankan ciyawa sai wata 'yar tsuntsuwa ta zo ta sauka a kan bishiya, ta tarar da 'yar yarinya. Sai ta fara waka tana cewa: Dan tsuntsu kar ka fada kan 'yar Sarki, Wadda kishiyoyi suka ce, Wai dan itace uwarta ta haifa,
Suka jefa ta kan bishiya, Ba dan itace ba ne , 'Yar Sarki ce." Ta rinka maimaita wannan waka, har bayin Sarki suka ji wakar 'yar yarinya ta kan bishiya. Wannan ya sa suka fita da gudu, suka koma gari.
Washe-gari ma da suka koma yankan ciyawa sai suka ji wakar. Da suka kasa kunnuwansu da kyau, suka kuma saurari wakar 'yar yarinya, sai suka koma gida suka gayyaci mutanen gari masu yawa, domin su ma su je jejin su ji. Mutanen gari suka saurari wakar da tsuntsuwa ke yi wa yarinya. Daga nan fa suka koma gari, suka je suka sanar da Sarki abin da suka ji. Sarki ya tashi da kansa ya nufi jeji inda yarinyar take, ya sa aka hau bishiya a ga ko me yake yin wannan waka.
Da aka hau bishiya sai ga yarinya kyakkyawa mai kama da Sarki, sai ka ce kakinta ya yi. Bayan an sauko da ita Sarki ya gan ta, nan da nan ya rungumi 'yarsa, yana ta salati irin na godiya ga Allah, yana sumbatar yarinyar nan, don
kauna irin ta 'ya da mahaifi.
Bayan wannan nuna murna ta Sarki da amsar barka da arziki daga Jama'arsa da ke wurin, sai ya sa aka kawo masa doki ya hau, aka mika masa diyarsa, suka hau doki tare, shi da dimbin jama'a suka kama hanyar gari.
Da suka isa gida sai ya aika aka kawo masa uwar yarinyar da aka kai can wani gida da ke bayan gari, yana cike da nadama, amma kuma a cikin muryar bayyana farin ciki, ya ba amaryar hakuri, ya nemi ta yafe masa horon da ya yi mata ba tare da laifinta ba, a sakamakon makircin kishiyoyinta.
Bayan fada ta cika ta batse da mutanen gari, sai aka bayyana musu miyagun halaye da makircin sauran matan Sarki, da yadda suka sa Sarki ya hori matarsa ba tare da ta yi masa laifi ba, da kuma yadda suka jefar da 'yar Sarki a daji. Nan take Sarki ya umarci Hauni da ya fille musu kawuna, aka je aka zuba su a rami, aka binne.
Sarki kuma ya ci gaba da sabuwar rayuwa shi da amaryarsa da "'yarsa.
Da ba domin Gizo ba da na shara muku karya.
Kurunkus.
Munciro wannan ne daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman