'Yan bindiga sun bude wuta a kasuwar 'Yan tumaki, sun kashe mutum 2, sun raunata mutune da dama a jihar Katsina
- Katsina City News
- 05 Apr, 2024
- 745
Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a kasuwar garin 'Yan tumaki da ke jihar Katsina inda suka hallaka mutum biyu, tare da raunata mutune da dama a yayin da suke tsaka da cin kasuwar.
Katsina Reporters ta samu cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na ranar nan, a yayin da ake tsaka da cin kasuwa, kuma a daidai lokacin da wasu ke haramar tafiya masallacin juma'a.
Majiyar ta ce 'yan bindigar basu ɗauki kowa ba, sai dai suka yi ta harbe harbe kan mai uwa da wabi wanda cikin mutanen da suka ka-she ciki har da mace 1 daga bisa ni suka ran ta ana kare.
Kasuwar Yantumaki na cikin karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina dai na ci ne a duk ranakun Juma'a a kowane mako.
Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani daga hukumomin tsaro game da wannan lamarin.