Yakubu Lado Ya Tallafa wa Dalibai, 'Yan Jarida, Matasa da sauransu
- Katsina City News
- 05 Apr, 2024
- 523
A cikin tallafin watan Ramadan ga kungiyoyi daban-daban a fadin jihar Katsina, fitaccen dan siyasa, Sanata Yakubu Lado Danmarke, ya raba tallafi ga kungiyoyin matasa da mata da dalibai da ‘yan jarida da sauran kungiyoyi da daidaikun jama'a a jihar Katsina.
Yan jarida da gidajen jaridu da kungiyoyi da dama sun samu tallafin, wanda hakan al'ada ce ta Sanata Yakubu Lado tsawon lokaci.
A cikin wannan watan na Ramadan, Sanata Lado ya bude daruruwan wuraren ciyarwa a fadin jihar inda ake raba dafaffen abincin da hatsi da kudi ga marasa galihu don rage radadin hauhawar farashin kayan abincin da sauran kayayyaki ga al'uma.
Wadanda suka amfana da wannan karimcin sun hada da ‘yan gudun hijira da marayu da zaurawa da masu bukata ta musamman da daruruwan dalibai da suka samu tallafin karatu.
Mafi akasarin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu, sun ce tallafin watan Ramadan da Sanata Lado raba ya fi wanda gwamnatin jihar Katsina ta raba.
Gwamnatin jihar Katsina dai tace ta kashe Naira biliyon goma (N10b) kan ciyarwa a watan nan na Ramadan.