Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta Ayyana Wasu Ayyukan Barna a Matsayin Haramun a Hukumance, tare da sanya Ido ga masu yi.
- Katsina City News
- 04 Apr, 2024
- 667
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Alhamis 4 ga watan Afrilu 2024 Hukumar ta Ayyana Wasan Gala, Kauranci (Sara suka) Kaɗe-kaɗen DJ, tare da soke shugabancin Kungiyar Hisbah da ba ta gwamnati ba.
Haka Zalika, Hukumar ta Haramta Yin wasu Al'adu a wajen Bukukuwa ba tare da Izini ba a rubuce, Izinin kuma zai biyo bayan aike da sako da bayyanawa hukumar yanda za'a gudanar da Al'adun bukukuwan don tantance wanda bai sabawa Shari'a da hankali ba.
Wadannan bayanai duka sun fito ne daga bakin Babban Kwamandan ta na jihar Katsina, Dakta Aminu Usman (Abu Ammar) a wajen taron wayar da kai da karama juna sani da hukumar ta shirya a bangarorin kungiyoyin Addinin musulunci da zasu yi aiki kafada da kafada da hukumar don yaki da Baɗala a jihar Katsina.
Taron da aka gabatar a babban dakin taro na ma'aikatar Kananan Hukumomin jihar Katsina ya samu halartar Gwamnan jihar Katsina wanda mataimakin sa Farooq Lawal Jobe ya wakilta, inda ya gabatar da jawabi a madadin Gwamnan jihar Katsina.
Tare da jawabin kwarin gwiwa daga bakin Babban Alkalin Alkalai na jihar Katsina, mai shari'a musa Danladi Abubakar, wanda ya bayyana cewa sunyi Nazarin Dokokin da suka kafa hukumar Hisbah babu inda tayi karo da Dokokin kasa ko na jiha wanda zai iya haddasa rashin jituwa tsakanin Al'umma.
Don haka Babban Alkalin ya bada Shawara kafa Kotun Tafi da gidan ka don gaggawar yanke hukumci akan duk wanda aka kama ya saba Doka, yace "idan akai haka zai sanya dole mutane su zamo masu da'a.
Manyan Malamai sun gabatar da Kasida akan Minene Hisbah, Asalinta da yanda yakama Dan Hisbah ya zama. Tare da Addu'o,i na fatan Alheri ga taron da Mahalarta taron da suka hada da Kungiyoyin Darika, Izala, Kur'aniyun da sauransu.