Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Mudi Da Ɗan Shi, Sun Baƙunci Lahira......
- Katsina City News
- 02 Apr, 2024
- 283
Wani faɗa ya ɓarke tsakanin ƴan ta'addar Ansaru da ɓangaren, Ɗan ta'addar daji Dogo Gide akan mallakar wuraren haƙar ma'adanai, faɗan da yayi sanadiyyar mutuwar mahara da dama daga kowane ɓangare.
Bayanan sirri na tsaro sun tabbatar da harin wanda ya faru ƙauyen Kuyello dake ƙaramar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna.
Ɗan ta'addar Mudi da Ɗan shi Murtala da suke ɓangaren Dogo Gide sun rasa rayukan su ta sanadiyyar wannan gumurzun da akayi akan wazai mallaki wurin haƙar ma'adanan dake yankin
An dai bayyana cewa akwai wuraren haƙar gwalagwalai da da dama a yankin Birnin Gwari waɗanda da dama Idan an haƙo su ake fita dasu Najeriya ba bisa ƙa'ida ba ta ɓangaren Jamhuriyar Nijar.
PRNigeria ta samu bayanai cewa kowane ɓangare an kashe mashi mabiyan da yawan gaske.
A wani ɓangaren kuma maharan sun kai hari a Gusau Babban birnin jihar Zamfara inda suka sace Mutane yayin da suke Sallahr tahajjud.
Daga shafin Muhammad Aminu Kabir