Ɗan Gidan El-Rufai Ya Caccaki Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna.
- Katsina City News
- 30 Mar, 2024
- 534
Bashir El-Rufai ya zargi Gwamnan jihar Uba Sani da kaucewa ayyukan da ya rataya a wuyansa ta hanyar kaurace wa jihar da zama a Babban birnin tarayya Abuja.
Bashir, dan Tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya kuma soki Gwamna Sani, abokin mahaifinsa, kan yadda ya dabaibaye kansa da wasu gungun mataimaka marasa cancanta da aka nada su kawai don neman goyon bayan siyasar sa.
Bashir ya kara da cewa, maimakon amincewa da gazawar Gwamnatinsa Uba Sani ta zabi kawar da sukar ne ta hanyar yin tsokaci kan bashin da ta gada daga Gwamnatin Gwamna El-Rufai.
Tun da farko Gwamna Sani ya bayyana a wani taro da aka yi a Kaduna cewa ya gaji bashin da ya kai $587m, N85bn, da kuma bashin kwangila 115 daga Gwamnatin El-Rufai, Wanda hakan ya sa ya fuskanci kalubalen biyan albashin ma’aikata.
To sai dai kuma a wani martani da ya mayar ga gwamnatin jihar Kaduna a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter jim kadan bayan haka, Bashir El-Rufai ya caccaki Gwamna Sani da tawagarsa, inda ya zarge su da rashin iya aiki, hauhawar farashin kwangila, da kuma hasashen Forex
Matashin Bashir El-Rufai ya bayyana cewa: “Wadannan mutanen sun gane cewa gaba ɗaya basu da kwarewa, Kuma hanya daya tilo da zasu iya boye rashin sanin ya kamata su ne su kawar da zargi. Gwamnan da kullum yana nan a Abuja bai san halin da jihar take ciki ba”
KBC Hausa