ZAMFARA NA BUKATAR KARIN YAWAN SOJOJI
- Katsina City News
- 26 Mar, 2024
- 413
@Katsina Times
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi kira da a ƙara yawan sojojin da za aka tura Jihar.
A ranar Litinin ɗin nan ne Gwamnan ya ziyxarci Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Christopher Gwabin Musa, a Hedikwatar tsaro da ke Abuja.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa Gwamnan ya gana da Babban Hafsan tsaron ne domin tattauna batun matsalar a jihar Zamfara.
A yayin taron, Gwamna Lawal ya bayyana damuwar sa kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare a wasu sassan Jihar Zamfara.
Ya kuma yi kira ga Babban Hafsan tsaron ƙasar da ya tura ƙarin sojoji da makaman da suka dace zuwa jihar.
“A yau na zo nan ne domin tattaunawa kan matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar Zamfara. Na zo nan a 'yan watannin da suka gabata saboda wannan batun.
“A ’yan kwanakin nan an sha fama da matsalar hare-haren ’yan bindiga a wasu yankunan jihar.
“A cikin makon nan an kai wani hari a Ƙaramar Hukumar Tsafe, wanda ya yi sanadin asarar rayuka, ciki har da Jami’in Rundunar Kare Jama’a "Askarawan Zamfara" (CPG), sannan wasu ’yan bindiga sun ƙona motocin sojoji da suka haɗa da na jami’an CPG.
“Muna fama da ƙarancin sojoji a Zamfara saboda an sake tura wasu jami’an yankin Arewa maso Gabas.
“Manoma ba sa iya noma gonakinsu, kuma hare-haren da ake ci gaba da kaiwa ya janyo asarar rayuka da dama.
“Ina so in yi amfani da wannan dama wajen kira gare ku da ku haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tura ƙarin sojoji zuwa Zamfara, irin wannan mataki na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro da kuma dawo da zaman lafiya a jihar.
“Tsarin jami’an tsaro babu shakka zai kwantar wa jama’a hankali tare da karya gwiwar masu aikata laifuka daga aikata munanan ayyukansu.
Da yake mayar da martani, Babban Hafsan tsaron ƙasa, Janar Christopher Gwabin Musa, ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Lawal na yaƙi da ’yan bindiga a Zamfara.
Ya ce: “Ina godiya ga ƙoƙarin da ka ke yi na yaƙar rashin tsaro. Muna shirin daidaita al'amura a Zamfara kamar yadda muka yi a Maiduguri.
"Muna tattaunawa da dukkanin Kwamandoji da masu ruwa da tsaki don magance matsalar hare-haren, wanda ke matuƙar sanya ɓacin rai," inji Janar Musa