"Rabon da Jami'an Tsaro su Kaimana Ɗauki Tun Lokacin Gwamna Masari" Al'ummar Shekewa sun Koka
- Katsina City News
- 25 Mar, 2024
- 547
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Al'ummar Garin Shekewa dake karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina sun koka akan halin ko Inkula da Gwamnati da jami'an tsaro sukayi da Rayuwar su, wanda hakan yayi sanadin da 'yan Ta'adda suka Tarwatsa garin baki daya. Inda suka bayyana cewa rabon da Jami'an tsaro su shiga garin suyi Batakashi da Barayi tun lokacin Gwamna Aminu Masari.
Garin Shekewa dake da Tazarar Kilomita Shida daga garin Batsari yana fuskantar Kalubale na 'Yan ta'adda wanda suka maida garin sansanin su. Bayan Kai wani Mummunan hari a ranar Talata da ta gabata 19 ga watan Maris wanda yayi sanadiyar Kashe Mutum bakwai, da bacewar Fiye da Mutum goma, da aka gaza Tantance Kashesu aka yi ko garkuwa akayi dasu.
"An kashe Magidanta Bakwai anyi Jana'izar Mutum Biyar biyu kuma ba'a iya dauko gawarsu ba saboda 'yan ta'addan sun mamaye garin" Inji wasu da sukayi karfin halin sauke Farilla Kifaya, akan Mamatan da 'Yan bindiga suka kashe.
"Tanimu, Sani mai Kero, Kabirun Malam Yunusa, Surajo, da Alhaji Manu." Sune Mutanen da aka samu yi musa Jana'iza bayan 'Yan Taddan sun kashesu.
Binciken Katsina Times ya gano cewa, Kauyuka hudu da ke zagaye da garin Shekewa, duka suna Karkashin Ikon 'Yan'adda, suke da cikakken Iko a garin Camɓala, Katoge, Umanare, da Kauyen Dantidu.
"Mun Faɗa wata Musiba, ta ɓangarori biyu, da Bangaren Jami'an tsaro, da Bangaren Ɓarayi, Idan Jami'an tsaro suka zo garin sai suyi ta bugun mu, suce muna hada kai da Barayi, akwai lokacin da suka kashe wani wanda baiji ba bai gani ba, da bindiga, daga baya suka bada hakuri bayan sun gano ba barawo bane. Haka kuma Barayi su shigo garin namu suna kashe mu, suna cewa muna tura masu jami'an tsaro." Inji wasu da muka tattauna da su.
Garin Shekewa da fiye da Mutum dubu uku (3000) ke rayuwa a cikinsa ya zama kufai, babu kowa a cikinsa.
Binciken jaridun Katsina Times ya gano cewa a ranar da Sojoji suka wuce da Shanun sata da suka kwato daga hannun Barayin Daji, ta garin na Shekewa a washe gari Barayin suka shiga garin suka Tarwatsa kowa da kowa, suka kashe na kashewa.
Irin Barnar da suke
Bayan da suka shiga garin sukai ruwan wuta kan mai uwa dawabi, suka kashe na kashewa sai suka bi gida-gida suna ɗebe duk wani abu da dan Adam ka iya amfani dashi ya rayu, madamar mai kyau ne, sai sun dauka, ragowar kuma su banka masu wuta.
"Rufin Daki na Kwano, Gadajen Mata, da Kyawaren Kofofi, duka sun kwashe sun tafi da su Daji, abinci dama ba'a magana" inji daya daga cikin wanda ya tsira da rayuwar sa da muke zantawa dashi.
Game da 'Yan Community Watch Corps C-WATCH da Gwamna Radda ya kafa don yakar 'yan Ta'adda, Mutanen Shekewa sun yaba, don kuwa sun ce, suna giftawa a yankin nasu, idan anyi sa'a su kamo daya ko biyu daga cikin barayin su harbe.
A halin yanzu dai Shekewa ta zama kufai, duk an tarwatse kowa ya nemi inda zai iya rayuwa, wasu Batsari Wasu sun mazaya Ruma, wasu kuma duka sun bar yankin zuwa inda suke fatan samun sauki.