Yadda Ɓarayin Daji Suka Halaka Mutane Goma Sha Biyu A Ƙananan Hukumomin Safana Da Batsari.

top-news


Muhammad Aminu Kabir 

A jiya Asabar 23/03/2024 ƴan bindiga suka kai mummunan hare-hare  a wasu ƙauyuka guda Ukku dake ƙananan hukumomin Safana da Batsari a jihar Katsina inda suka halaka Mutane

Ƴan bidigar dai ɗauke da miyagun makamai sun kai hare-haren ne a jiya Asabar da misalin ƙarfe Goma sha Biyu 12:00pm na rana inda suka kashe kimanin Mutane Goma Sha Biyu 12 a ƙauyukan KUKAR RABO da TAKA LAFIYA cikin ƙaramar hukumar safana, yayinda kuma a ƙauyen TORAWA dake ƙaramar hukumar Batsari nan ma suka kai farmaki tare da kashe wasu Mutanen.

Wani Mazaunin yankin ya bayyana mana cewa a Kukar Rabo ɓarayin sun kashe Mutan Bakwai yayinda a ƙauyen Taka-lafia kuma suka kashe Ukku 3, Sai Torawa nan ma suka kashe mutum Biyu 2, jimillar Mutane Goma Sha Biyu kenan da suka rigamu gidan gaskiya sanadiyyar wannan harin ta'addancin.

Kazalika ya ƙara da cewa kawo yanzu anyi jana'izar wasu a cikin garin Batsari, wasu kuma anyi jana'izar a can ƙauyukan nasu bayan da Jami'an tsaro sukaje aka gano wasu gawawwakin

Kawo lokacin haɗa wannan rahaton bamu samu wani ƙarin bayani daga jami'an tsaroba kan faruwar wannan Lamarin.

Ko jiyan dai a ƙaramar hukumar Faskari wajen Mairua ɓarayin sun kai farmaki yayinda Mutane suke tsaka da Sallahr Tarawihi inda suka kashe wani fitaccen attajiri a yankin.

A Ɗan tsakanin nan dai ɓarayin sun zafafa kai munana hare hare musamman a yankunan jihohin Katsina da Zamfara inda suke kisan wulaƙanci tare da ƙone ƙonen garuruwa da kayan Abincin jama'a.

Sai dai masana harkar tsaro na ganin cewa ɓarayin suna samun matsine daga Jami'an tsaro shiyasa suke kai ire iren waɗannan hare haren domin su nuna har yanzu suna da ƙarfin su.

A kullum dai Adduar da muke itace Allah duk masu hannu a cikin wannan Lamarin na rashin tsaro Allah kayi maganin su

NNPC Advert