Kungiyar Kwararrun Masu Zanen gine-gine ta Ƙasa, Nigerian Institute of Architects (NIA) Ta shirya walimar Shan Ruwa a Katsina
- Katsina City News
- 24 Mar, 2024
- 740
Kungiyar Kwararrun Masu Zane ta Ƙasa, Nigerian Institute of Architects (NIA) Ta shirya walimar Shan Ruwa a Katsina
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Asabar 23 ga watan Maris daidai da kwanan watan Azumin Ramadan 13 ga wata, Nigerian Institute of Architects bisa jagorancin Shugabanta na jihar Katsina Architect Kamaladeen Dahiru suka shirya gagarumin Shan Ruwa (Buda Baki) tare da sauran 'Ya'yan Kungiyar, 'Yan'uwa da Abokanan Arziki a Babban wajen cin abinci na Katsina Motel dake cikin birnin Katsina.
A wajen Taron Anci an Sha, anyi Addu'o'i wa Ƙasa da jihar Katsina domin neman Zaman Lafiya da kawo karshen matsalolin Tsadar Rayuwa.
Da yake bayyana Makasudin Architect Kamala Kuma shugaban kungiyar ta NIA a jihar Katsina ya bayyana cewa, shi wannan tsarin na Iftaar (Shan ruwa) kungiyar tana shirya shi duk shekara a ƙasa ma baki daya ba a jihar Katsina ba domin haduwa, sada zumunta da Addu'a duba da watan karbar Addu'a ne. Yace "a jihar Katsina ma muna shirya irin haka a matakin jiha, saidai abin ya samu cigaba fiye da ko wace shekara, a Mafiya yawan lokuta muna yi a cikin gida ne, kuma wasu daga cikin 'ya'yan kungiyar suke daukar nauyi."
Yace "Kamar wannan na wannan shekara muna jinjina da yabawa ga Honorabul Danmajalisar Tarayya Rimi, Charanci Architect Murtala Ibrahim Banye da ya dauki nauyin shirya taron, yace duk da baya kasar ya tafi Umra, amma ya bada duk gudumawar da ake bukata wajen shirya buda bakin."
Shima Architect Abdulsalam Maiyadi ya yaba da shirya wannan taro na zumunci da ya tattaro yayan kungiyar ta NIA kuma aka sada zumunci da Addu'o'i yace wannan ba karamin alheri bane, kuma ya motsa kungiyar sosai duba da a watan Ramadan wasu ayyuka suna raguwa domin Tunkarar Ibada gadan-gadan."
Taron da ya gudana a Dakin cin abinci na Katsina Motel an raba Al'quranai ga dukkanin Mahalarta taron da kuma addu'o,i ma jihar Katsina da kasa baki daya.