Hukumar Hana Fasa Kwabri a Nijeriya Ta Soke Amsar Harajin Kaso 25% Na Motocin da Aka Shigo Da su ba akan Ka'ida ba
- Katsina City News
- 22 Mar, 2024
- 525
Yanzu Yanzu: Hukumar Dake Kula Da Hana Fasa Ƙwabri Ta Ƙasa Ƙwastam Ta Soke Karɓar Harajin Kaso 25% Na Motocin Da Aka Shigo Dasu Ba Bisa Ƙa'ida Ba A Najeriya.....
Haraji dai na zaman wasu kuɗaɗe ne da ƴan ƙasa suke biya domin samun kuɗaɗen shiga ga Gwamnatin Tarayya ko na Jihohin ko kuma na ƙananan hukumomi.
Hukumar a ta bakin mai magana da yawun ta Abdullahi Maiwada ya bayyana cewa bisa umarnin gwamnatin tarayyar Najeriya ƙarƙashin Ministan Ma'aikatar kuɗi da tattalin arzikin ƙasa ta Tarayya, ta fito da wani tsari domin sauƙaƙa ma Al'umma su iya biyan kuɗin harajin kayan da suka shigo dasu ba bisa ƙa'ida ba.
Ma'aikatar ta fitar da ƙwana Chas'in da zai fara daga 4th March 2024 har zuwa 5th July 2024
domin Mutane suje su biya kuɗin harajin su tare da gyara duk wasu takardun su cikin Sauƙi.
Maiwada a jawabin shi yace laakari da yanayin matsin tattalin arzikin da ake fama dashi yasa Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan Kuɗin ƙasar ya amince da soke harajin kashi Ashirin da Biyar 25% na "penalty" da aka sanya akan dukkanin wasu motoci da aka shigo dasu gida Najeriya.
Da wannan ake kiran masu ruwa da tsaki a harkar shigo da motoci da ƴan kasuwa da suyi amfani da wannan damar wajen zuwa su biya harajin kayan su domin su karɓi abin su kafin cikar ƙwanaki Chas'in da aka ware.
A jawabin shi ya ƙara da cewa ƴan ƙasa su sani hukumar bata da wani aiki illa cika Umarnin da Shugaban ƙasa yabata na karɓar Haraji, idan yanzu Gwamnati ta ce kada a amshi harajin kowa hukumar bata da hurumin ta karɓi haraji a wurin kowa.
Wuraren da hukumar ta ware domin biyan kuɗin harajin sun haɗa da Zone A jihar Lagos, Zone B Jihar Kaduna, Zone C jihar Rivers PortHacourt da Zone D jihar Bauchi.